Ƴan sanda sun kama ɗan kasuwa da ake zargi da yi wa ƙaramar yarinya ciki a Kano

‘Yan sanda daga Hedikwatar tsaro dake Bompai a Kano, a jiya Talata sun kama ɗan kasuwan nan Alhaji Ibrahim wanda ya yi wa wata ƙaramar yarinya mai shekaru 14, Humaira Ado  ciki.

Tun da farko Alhaji Ibrahim ya yi ƙaran iyayen yarinyar kotun Shari’ar musulunci da ke Kano, a ƙokarin sa na karkatar da hankali tare da lalata shari’ar, amma daga karshe an kama shi a jiya Talata, duk da cewa an ba shi dama don komawa gida ya dawo da safiyar yau.

  • Ƴan sanda sun kama ɗan kasuwa da ake zargi da yi wa ƙaramar yarinya ciki a Kano
  • Kasuwancin zamani na da tasiri a ɗorewar tattalin arziƙin zamani- Shugaban NITDA

Wakilin iyayen yarinyar wanda ya yi magana da Mujallar Neptune Prime ta fara fitar da labarin, a wayar tarho ya ce yayi mamakin yanda aka kasa samun wata kafar yaɗa labarai a jihar Kano da ta bibiyi wannan lamari.

Ya yi ƙira ga Lauyoyin masu kare Haƙƙin Dan -Adam, Gidajen yaɗa labarai, kungiyoyi masu zaman kansu, Mata Lauyoyi, da su sanya idanu akan wannan shari’ar don gudun kada wasu manyan mutane su nemi kashe maganar.

Ya ce mafi muni shine wanda ya yi wabyarinyar nan wannan ta’asa suna da dangantaka ta jini domin yana matsayin mahaifi ne a gareta. Ya ce a halin yanzu Humaira tana cikin damuwa, bata iya cin abinci kullum cikin  kuka kada hakan ya shafi lafiyarta.

An wallafa wannan Labari September 22, 2021 5:30 PM