‘YAN BINDIGA: An hana siyar da fetur a jarka a Jigawa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta haramta siyar da man fetur a jarka a duk fadin Jihar a yunkurinta na dakele ayukan yan bindaga.

Gwamnatin ta bayyana sabon dokar ne bayan samun yawaitar ayukan masu garkuwa da Mutane a fadin Jihar.

Jaridar PREMIUM TIMES HAUSA ta ga Yadda gwamna Muhammad Badaru ya sanya dokar hannu a wata takardar dake bada umarnin nan take.

Dokar ta ce ba’a yarda ba masu gidan mai su siyar da fetur a cikin Jarka har fiye da lita 60 sai dai ga ma’aikatar gwamnati ko kuma ma’aikata masu zaman kansu da gwamnati ta amince da da su.

gwamnatin ta kuma haramta sana’ar acaba da daddare daga karfe 10 zuwa 6 na safe a fadin Jihar baki daya.

Kakakin Yan Sanda a Jihar Jigawa Lawan Adam, yace jami’an tsaro sun shirya tsab wajen tabbatar da dokar ta gwannati domin kare Jihar daga mugun iri.

Dama a baya PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito yadda Gwamna Badaru ya gargadi shuwagabanin Fulani na Miyatti Allah dasu daina baiwa bara gurbin matasan wajen zama a fadin Jihar.

Ana zargin yan bindaga dake gujewa fushin soja a Jihar Zamfara suna kwararuwa makwabtan Jihohi ciki har da Jigawa. Jihar ta Jigawa dai an santa da zaman lafiya da numa da Noma da kiwo.