SHUGABANCIN NAJERIYA: A koma tsarin karɓa-karɓa, kowane yanki ya yi mulki shekaru huɗu kacal ya sauka -Ekweremadu

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu ya bada shawarar a yi wa kundin mulkin Najeriya na 1999 kwaskwarima, a maida tsarin mulki ya zama karɓa-karɓa.

Idan an an koma karɓa-karɓar ma, Ekweremadu cewa ya yi a yi watsi da bada damar yin zango biyu ga shugaban ƙasa.

Ya ce kawai idan ɗan wannan shiyya ya yi shekarun sa na huɗun zangon farko, sai ya sauka a zaɓi ɗan wani shiyya shi ma ya shekara huɗu ya sauka.

Ekweremadu ya yi wannan shawara ce a lokacin da ya ke jawabi wurin taron Makon Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa Reshen Ikeja a Lagos.

Ya ce tun tuni ya sha bada shawara cewa a koma tsarin yin shugabancin karɓa-karɓa na zangon shekaru biyar ko shida kaɗai.

“Yin hakan zai kawar mana da kawar da hankulan jama’a, ƙumbiya-ƙummbiyar dole sai an ci zaɓe zango na biyu, zai ɗinke ɓarakar rashin haɗin kan ƙasar nan.

“Hakan kuma zai sa a riƙa sauya akalar mulki daga wannan yanki zuwa wannan, ba tare da wani yanki ya riƙa ƙorafin cewa an tauye masa damar sa ba, ƙasar yadda ke faruwa a yanzu ba.

“Matsawar kowane yanki ya amince kuma gani ƙuru-ƙuru cewa idan wannan yanki ya kammala zangon sa su ma za su karɓa su yi, to za a daina tayar da jijiyoyin wuya wajen neman shugabanci bakin-rai-bakin-fama.

“Sannan kuma ya fi zama alheri gwamna ko shugaban ƙasa ya san cewa zango ɗaya ne kacal ya ke da damar da zai yi wa jama’a duk ayyukan da zai iya yi ya kammala kafin ya sauka.”