ZAZZABIN LASSA: Mutum 247 sun kamu, 50 sun mutu a Najeriya

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa mutum 247 ne suka kamu da zazzabin lassa a kasar nan.

NCDC ta kuma kara da cewa a wannan shekara cutar ta yi ajalin mutum 50 a Najeriya.

Cutar ta yadu zuwa kananan hukumomin 52 dake jihohi 14.

Zuwa yanzu jihohin Ondo da Edo ne suka fi fama da yaduwar cutar.

Mutum 69 sun kamu, mutum 19 sun mutu a jihar Ondo.

Sannan mutum 108 sun kamu kuma mutum 12 sun mutu a jihar Edo.

Jami’in gudanar da bincike na ma’aikatar lafiya ta jihar Edo Steven Fagbemi ya ce zazzabin lassa ta fi yaduwa a shekarar 2021 fiye da shekarar 2020.

Fagbami ya ce hakan ya faru ne saboda yadda kasan ta maida hankali wajen dakile yaduwar cutar korona sannan da rashin iya tanttance zazzabin lassa da cutar korona da mutane suka yi fama da shi wanda hakan kan hana su zuwa asibiti da wuri.

Matakan Kiyaye Kamuwa Da Zazzabin Lassa

1 – A raba beraye daga cikin gida: Kada a yi sakaci har beraye su samu wurin zama a cikin gida.

2 – A toshe duk wani rami a gida: Beraye daga wani gida kan shigo maka su boye, idan ka bar ramu a cikin gidan ka.

3 – A rika barin abinci ya dahu sosai: A rika cin abin da aka dafa ya dafu sosai.

4 – A guji taba mataccen bera ko mai rai da hannu: Taba mataccen bera ko mai rai da hannu na iya sa a kamu da cutar Zazabin Lassa.

5 – A rika yawaita tsaftace gida da kewayen sa: Barin datti a gina na kawo beraye ko daga waje ko daga wani gida.

6 – A guji cin kayan marmarin da bera ya gutsira: Wannan ganganci ne sosai, don haka a guji ci ko da kuwa an wanke.

7 – A rika ajiye abinci a wuri mai murfi: Bri abinci a bude kan kai bera ya ci, kuma har yayi fitsari ko kashi a kai.

8 – A rika rufe kwandon zuba shara: Beraye na buruntu cikin kwandon shara, su na cin sauran abincin da aka zubar.

9 – A rika wanke hannu da sabulu da ruwa mai tsafta: Dama wannan na cikin matakan farko na tabbatar da tsafta a jikin mutum.

10 – A rika garzayawa asibiti idan babu lafiya: Garzayawa asibiti ya fi a tsaya ana kame-kamen shan magani a gida.

11 – A daina shanya abinci a waje kuma a bude a kasa: Barin abinci a bude illa ce, sannan shanya abinci a kasa ko a kan dabe kan haifar da cututtuka.

12 – A guje kusantar wanda ya kamu da cutar: Likita ne kadai zai iya kusantar wanda ya kamu da zazzabin lassa. Don haka a kiyaye.