Za a rataye duk wanda aka samu da taimakawa masu garkuwa a jihar Neja

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya sanya hannu a wasu dokoki ciki har da na rataye duk wanda aka kama da laifin taimakawa masu garkuwa da mutane da satar dabbobi a jihar.

Wannan na ƙumshe ne a cikin watan sanarwa da jami’ar watsa labaran gwamnan Mary Noel-Barje ta fitar ranar Juma’a.

Ta ce da yake ƙarin haske game da sabbin dokokin da kuma waɗanda aka yi wa kwaskwarima a majalisar dokokin jihar dake Minna, Gwamnan ya ce dokar hukunta masu garkuwa da mutane da satar dabbobi na 2016 da aka yi wa kwaskwarima zai hukunta masu taimakawa barayin shanu da satar mutane a jihar.

Ya ƙara da cewa, duk ɗan leƙen asirin ƴan ta’addan da aka kama zai fuskanci hukuncin kisa ta hanyar rataya a bainar jama’a.

A cewarsa, yanzu doka ta tanadi “duk wanda aka kama an haɗa baki da shi aka yi garkuwa da wani ko aka sace dabbobin wani, ko aka samu wani yana taimakawa masu garkuwa da mutane ko barayin shanu, hukuncinsa shine kisa ta rataya”.

Gwamna Sani Bello ya ce matakin ladabtarwar abin yabawa ne kuma ya zama wajibi idan aka yi la’akari da kalubalen tsaro da ke ci gaba da yin barazana ga zaman lafiyar jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Ya yi Allah-Wadai da masu taimakawa ƴan ta’adda ta hanyar leƙen asiri waɗanda, a cewarsa, sun ba da gudummawa wajen dakile ƙoƙarin jami’an tsaro na yaƙi da ƴan ta’adda.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, dokar ƴan sa kai (Vigilante) ta 2021 da aka yi wa kwaskwarima an yi ta ne don ingantawa tare da ƙarfafa ƙungiyar ƴan sa kai ta jihar don yin aiki bisa tsarin doka a yayin da suke taimakawa jami’an tsaro na ƙasa wajen yaƙi da ƴan ta’adda.

Gwamna Sani Bello ya kuma bayyana cewa, yana da yaƙini sa hannu kan Dokar Hukumar Kula da Ayyukan Majalisar Dokoki ta jihar da ya yi zai ƙara inganta ayyukan Ƴan Majalisar da kuma tabbatar da haɗin kan da ke akwai tsakanin bangaren Zartarwa da na Majalisar.