Hukumar Bin Diddigin Safarar Kuɗaɗen Sirri NFIU ta ce ta na shan matsin-lamba daga ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamanti

Hukumar Bin Diddigin Safarar Kuɗaɗen Sirri, wato National Financial Intelligence Unit (NFIU) ta ce ta na fama da shan matsin-lamba daga manyan masu riƙe da muƙaman siyasa da manyan jami’an gwamnati masu neman bayanai ba bisa ƙa’idar doka ba gaba wajen NFIU ɗin.

NFIU ta yi wannan bayani ne cikin wata sanarwa da ta buga a ranar Labara, mai taken ‘Shawara Ga Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa Da Manyan Jami’an Gwamnati.”

“Ya zama wajibi mu nuna ɓacin rai dangane da yadda manyan masu riƙe da muƙaman siyasa da manyan jami’an gwamnati ke kauce wa hanya ba bisa ƙa’ida ba, su na karambanin tambayar wasu bayanai na sirri daga Hukumar NFIU.”

Jami’in Yaɗa Labarai na NFIU, Ahmed Dikko ne ya sa hannu a kan sanarwar.

“NFIU hukuma ce wadda doka ta kafa, kuma ba ta da hurumin miƙa wani ko wasu bayanai na sirri ayyukan ta, sai jami’an tsaro da hukumomin kula da wasu ayyukan hada-hadar da ba bisa ƙa’ida ba da ke cikin ƙasashe fiye da 170 na faɗin duniya.”

“Don haka mu na sake jaddada cewa NFIU ba ta bayyana wasu bayanai na sirri ga jami’an gwamnati ko masu riƙe da muƙaman siyasa ko don wani dalili na hada-hadar kasuwanci.

Dikko ya ƙara da cewa, “NFIU ta gargaɗi dukkan ma’aikatan ta cewa kada wanda ya kuskura ya miƙa wasu bayanai ga ‘yan siyasa ko jami’an gwamnati.”

“Duk wanda aka kama ya bayyana wani sirri, to daka za ta hau kan sa ta yi masa hukunci.”

Hukumar NFIU dai ta na a ƙarƙashin Babban Bankin Najeriya ne, CBN.

Ita ce sashen da ke tsara ayyukan bin diddgin harƙallar kuɗaɗen sata da badaƙala ko kuɗaɗen da ake ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga cikakken rahoton yadda aka kori Jami’an Hukumar Bin Diddigin Safarar Kuɗaɗen Sirri saboda sun zaƙalƙale wajen zurfafa binciken Atiku da Tinubu.

Wasu Jami’an Hukumar Bin Diddigin Safarar Kuɗaɗen Sirri’ wato National Financial Intelligence Unit (NFIU) sun rasa aikin su saboda zaƙalƙalewar da su ka riƙa yi wajen zurfafa binciken safarar kuɗaɗen Atiku Abubakar da Bola Tinubu.

Atiku da Tinubu dai duk ana kyautata masu zaton tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Babban Daraktan NFIU, Modibbo Tukur ne ya aika wa manyan jami’an biyu takardun sallamar kowanen su daga aiki, a ranar 29 Ga Yuni, kamar yadda PREMIUM TIMES ta tabbatar.

Majiyoyin PREMIUM TIMES sun nuna damuwar cewa korar da aka yi wa jami’an biyu kwata-kwata ba bisa ƙa’ida aka yi ta ba.

Cikin 2020 PREMIUM TIMES ta buga cikakken labarin yadda aka dakatar da Daraktan Binciken Sirri Mohammed Mustapha da kuma Daraktan Tantancewa Fehintola Salisu, kuma Mohammed Tukur ɗin ne dai ya dakatar da su a lokacin.

An dakatar da su ne saboda sun yi gaban-gabarar zurfafa binciken safara da hada-hadar kuɗaɗen Atiku Abubakar da Bola Tinubu, ba tare da sanin hukuma ba.

Sauran zarge-zargen da Tukur ya yi wa korarrun jami’an sun haɗa da:

1. Mustapha ya yi shisshigin rubuta wa Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya da Shugaban EFCC wasiƙa a kan wasu hada-hadar Atiku Abubakar, ba tare da Hukumar NFIU ce ta sa shi ba.

An ce wannan babban laifi ne matuƙa. Tukur ya ce hukumar NFIU ba ta ɗora alhakin binciken ayyukan hada-hadar Atiku a kan Mustapha ko ofishin sa ba.

Tukur ya kuma zargi Mustapha da aika wasiƙa ta neman waɗansu bayanai da ake zargin Tinubu da aikatawa a Amurka, maganar da tsohon batu ne.

Tsohon rikici ne wanda cikin 2011 CCB ta zargi Bola Tinubu da laifin buɗe asusun ajiya bankunan ƙasashen waje a lokacin da ya ke Gwamnan Legas daga 1999 zuwa 2007.

Sai dai kuma Kotun CCT ta kori ƙarar daga baya.

Tukur ya ce dukkan abubuwan da jami’an biyu su ka aikata, ba su nemi amincewar sa ko shawarar sa ba, a matsayin shi Tukur na Shugaban su kuma Shugaban NFIU.

Majiya ta ce tun a ranar 11 Ga Agusta Tukur ya aika masu da takardar dakatarwa da kuma gargaɗi kan binciken Tinubu da Atiku ba tare da an sa su ba.

Wata majiyar ta tabbatar wa PREMIUM TIMES Hausa cewa sai da aka bai wa su biyun ɗin da aka kora damar kare kan su tukunna.

Yadda Mustapha Ya Ƙara Kira Wa Kan Sa Ruwa:

Sannan kuma an samu Mustapha da laifin haɗa baki da wani jami’in NFIU, ya riƙa karɓar albashin sa a lokacin da aka dakatar da shi.

Cikin takardar korar Mustapha an gargaɗe shi tare da umarnin ya gaggauta maida wa Gwamnatin Tarayya dukkan albashin sa da ya bi ta ɓarauniyar hanya ya karɓa a lokacin da aka dakatar da shi.

Wakilin mu ya tuntubi Mustapha da Salisu ta waya amma ba su ce komai ba. Hatta saƙon tes da aka yi masu ma ba su bada amsa ba.

Idan ba a manta ba, wani ofishin lauya na C. Chris Ekemezie & Associate ya rubuta wa ICPC ƙorafi tare dai kai ƙarar Tukur, a kan dakatarwar da ya yi wa jami’an biyu.

Lauyan ya ce “an kori jami’an biyu ne saboda sun yi ƙoƙarin saɓule wa Atiku wando a ga irin safarar kuɗaɗen sirrin da ya ke yi.”

Masana da masu sharhi da dama na ganin korar akwai siyasa a cikin ta. Sannan kuma ba a kore su bisa ƙa’ida ba.