YUNƘURIN ƘAFA DOKAR HANA YANKA JAKUNA: Yadda aka hau sama tsakanin Kwamitin Majalisar Dattawa da dillala jakuna

An yamutsa gashin baki tsakanin mambobin Kwamitin Majalisar Dattawa masu lura da Ayyukan Noma da Bunƙasa Karkara, su da Ƙungiyar Dillalan Jakai na Ƙasa a ranar Litinin.
Lamarin ya faru ne a wurin zaman sauraren ra’ayoyin jama’a dangane da ƙudirin neman kafa dokar da za ta haramta kama jakai barkatai ana kamawa.
Ƙudirin wanda Sanata Abdullahi Yahaya daga Kebbi ya bijiro da shi, ya nemi a kafa dokar da za ta ayyana kare jakuna daga ƙarewa a ƙasar nan, saboda yanka su da ake yi, ana safarar fatocin jakan zuwa ƙasashen waje.
An dai gayyato masu ruwa da tsaki a harkar ciniki, safara da yanka jakunan domin a ji ƙarin haske a wajen su har a samu daidaito wajen kafa dokar.
Tuni aka yi wa ƙudirin karatun farko a cikin Yuli, 2021.
An yi ƙorafin cewa idan ba a gaggauta kafa dokar da za ta sa ƙa’idar yanka jakuna barkatai, to Najeriya za ta ci gaba da narka asarar rashin cin moriyar jakunan a cikin ƙasar nan.
Yayin da wasu ke cewa a hana yanka jakunan kwata-kwata, wasu na ganin cewa gara dai a shimfiɗa ƙa’idoji a dokance.
Shi kuwa Shugaban Ƙungiyar Dillalan Harkar Jakuna na Ƙasa (DDA), Ifeanyi Dike, ya yi gargaɗin cewa idan aka haramta yanka naman jakuna, to waɗanda za a karya wa jari da karya sana’o’in su za kai mutum miliyan 3. Wasu za su yi asarar harkokin su, wasu jarin da su ka zuba, wasu kuma hada-hadar su.”
Dike ya ce haramta yanka naman jakuna ba shi ne zai bunƙasa tattalin arzikin ƙasar nan ba.
Ya ce idan aka haramta, to za a samu bayyanar masu fasa-ƙwaurin jakunan ana yankawa ana kai fatun Chana.
“Don me za a tsani jakuna a ce wai idan ana ci gaba da yanka su za su ƙare. Ya aka yi shanu da ake yanka aƙalla 50,000 a kowace rana, ba su ƙarewa sai jakai da ake yanka waɗanda ba su kai yawan shanun da ake yankawa ba a kullum.”
Shi kuwa Ɗan Majalisar Tarayya Mohammed Datti, cewa ya yi ƙudirin ya na da amfani, a hana yawan yanka jakuna ana safarar fatun zuwa Chana, ana magani da su.
Shugaban Kwamitin, Sanata Bima Enagi, ya ce za a ci gaba da karɓar shawarwari daga jama’a.