CUTAR KURARRAJIN BIRI: Mutum 8 sun kamu a jihar Edo

Ma’aikatar kiwon lafiyar jihar Edo ta bayyana cewa mutum takwas sun kamu da cutar Monkey pox a jihar.

Gwamnati ta yi kira ga mutane da su kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin hana yaduwar cutar a jihar.

Kwamishinan kiwon lafiyar jihar Akoria Obehi wace ta sanar da haka wa manema labarai a garin Benin ranar Litini ta ce ma’aikatar ta aika da ma’aikatanta tare da daukan matakai domin dakile yaduwar cutar.

Obehi ta ce mutum takwas din da suka kamu da cutar duk sun warke kuma an sallame su.

Ta ce ya zama dole a wayar da kan mutane game da cutar domin kare su daga kamuwa da cutar.

“Monkey pox cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin yin cudanya da cin naman dabban da ya kamu da cutar irin su birai, bera da sauran su.

“Alamun cutar sun hada da zazzabi, ciwon kai, kumburin mukamuki, rashin karfin jiki, Jin zafi a makogoro, fesowan kurarraji da sauran su.

“Cutar kan dauki tsawon makonni biyu zuwa uku kafin a ga alamun cutar a jikin mutum sannan baya ga kamuwa da cutar daga jikin dabobbi ana iya kamuwa da cutar a jikin mutum wanda ke dauke da cutar.

“A guji yin mua’mula da dabbobi musamman wadanda suka kamu da cutar sannan a rika dafa naman ya dahu sosai sannan a yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu.

Cutar Monkey Pox ta zama annoba a duniya – WHO

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta sanar cewa cutar kurarraji na Monkey pox ya za annoba a duniya.

Shugaban kungiyar Tedros Ghebreyesus ya sanar da haka duk da cewa kwamitin da WHO ta kafa domin dakile yaduwar cutar ta yanke shawaran cewa yaduwar cutar bai kai matsayin da zai zama annoba ba.

A ranar 26 ga Yuni 2022 adadin yawan mutanen dake dauke da cutar ya kai 3,040 a kasashe 47.

Duk da haka kwamitin dakile yaduwar cutar ta duniya ta ce cutar bai kai matsayin annoba ba.

Zuwa yanzu cutar ta yadu zuwa kasashen 75 a cikin ‘yan makonni inda hakan ya sa cutar ta zama annoba.

Ghebreyesus ya ce ya fitar da sanarwan ne domin yin haka zai taimaka wajen daukan matakan da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar.

Ya ce ware kudade domin gudanar da bincike, gudanar da bincike, yin allurar rigakafi da yin wa mutane gwajin cutar na daga cikin matakan dakile yaduwar cutar.