‘Yan sanda sun kama barawon da ke wafce kudin baiko a coci ba a sani

Rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti ta kama wani barawon kudaden bakon da mutane suka tara a wani coci dake jihar Osun.
Kakakin rundunar Sunday Abutu ya sanar da haka yana mai cewa rundunar ta kama barawon da tsabar kudi har Naira 600,000.
Abutu ya ce barawon ya tabbatar wa rundunar cewa shi ne ya sace kudaden sannan za a kai shi kotu da zarar an kammala gudanar da bincike akai.
Bayan haka kakakin rundunar ta ce jami’an tsaro na ‘yan sanda sun kama wasu mutum 18 da ke aikata laifuka dabandaban a fadin jihar.
Ya ce an kama wadannan bisa laifukan da suka hada da sata, shiga kungiyar asiri, fashi da makami, garkuwa da mutane da dai sauran su.
Abutu ya ce rundunar ta yi nasarar kama wadannan mutane a dalilin samun hadin kai daga mutanen jihar da suka bai wasu jami’an tsaron yaki da miyagun mutane a fadin jihar.
Ya ce an kama su da na’urar janareta manya guda biyu, tufafi, takalma da kudi.
Abutu ya ce rundunar za ta kai mutanen kotu da zarar ta kammala bincike akan su.