Majalisar Dattawa ta amince da sunayen sabbin Kwashinonin Zaɓe, duk da ƙorafin cewa cikin su akwai ‘yan siyasa

A ranar Laraba ce Majalisar Dattawa ta amince da sunayen mutane 19 waɗanda Shugaba Muhammadu Buhari ya aika, a matsayin Kwamishinonin Zaɓe (REC).
Tun cikin watan Yuli Buhari ya naɗa su kuma ya aika sunayen a Majalisar Dattawa, inda ya nemi ta amince da su.
Daga cikin sunayen 19, biyar sun kammala wa’adin shekaru biyar, amma Buhari ya sake naɗa su domin su ƙara wa’adin wasu shekarun biyar, kuma wa’adij ƙarshe.
Sauran 14 kuma duk sabbin naɗi ne.
A cikin sabbin naɗin ne ƙungiyoyin rajin kare haƙƙin jama’a su ka riƙa rubuce-rubucen ƙorafe-ƙorafe cewa biyar a cikin su ba su cancanta Buhari ya naɗa su ba.
A cikin biyar ɗin, an zargi wasu da cewa ‘yan jam’iyyar APC ne, wasu kuma an zarge su da aikata harƙalla da cuwa-cuwa a baya.
Majalisar Dattawa ta amince da sunayen gaba ɗaya bayan Kwamitin Majalisar Dattawa mai lura da INEC ya kammala tantance sunayen.
Sai dai kuma majalisar ta ce ta amince da sunayen bayan ƙungiyoyi masu ƙorafi sun kasa gabatar da ƙwararan hujjojin zargin da su ke yi wa mutanen biyar.
“Masu zargi sun ƙi kawo takardar rantsuwar kotu (court affidavit) da sauran hujja mai tabbatar da wasu ‘yan APC ne, wasu kuma tsoffin ‘yan harƙalla ne.” Inji majalisa.
Ko a cikin makon makon jiya, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda INEC ta ƙi hukunta APC, PDP da sauran jam’iyyun da su ka karya dokar zaɓe a 2019.
Binciken ƙwaƙwaf ɗin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta kammala bayan zaɓen 2019, ta tattara bayanan yadda APC da PDP su ka karya dokokin ƙa’idar adadin kuɗaɗen da INEC ta amince su kashe tun daga yaƙin neman zaɓe.
Sashen Bin Diddigin Kashe Kuɗaɗen Jam’iyyu da ke ƙarƙashin INEC, ya ce Dokar Kashe Kuɗaɗen Jam’iyyu Sashe na 91 na 2010, ya gindaya cewa kada jam’iyya ta kashe fiye da naira biliyan 1 a lokacin kamfen.
“Amma a zaɓen 2019 APC ta kashe biliyan 4.6, adadin da ya kai N4,620,144,784.
“PDP ita ma ta kashe naira biliyan 3.2, adadin da ya kai N3,282,226,642.”
Sashen Bin Diddigin ya ce APC da PDP sun nunka adadin da doka ta amince a kashe har sau uku kenan.
Sai dai kuma fiye da shekaru uku bayan INEC ta fitar da wannan sanarwar karya doka, har yau na ta sake cewa komai ba.
Wata Dokar Da APC Da PDP DA Sauran Su Ka Karya:
Dokar Zaɓe a Sashe na 92(3) ta 2010, ta ce tilas kowace jam’iyya ta kai wa INEC rahoto uku na waɗannan kuɗaɗe na ta.
1. Kuɗaɗen gudummawar tara kuɗaɗen kamfen da ta samu. Ana so ta aika rahoton adadin watanni uku bayan zaɓen shugaban ƙasa.
2. Adadin kuɗaɗen da ta kashe a zaɓen shugaban ƙasa. Ana so jam’iyya ta kai wa INEC rahoton watanni shida bayan bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.
2. Adadin kuɗaɗen da ta kashe a duk shekara-shekara.
Sai dai kuma shekaru uku bayan kammala zaɓen shugaban ƙasa na 2019, jam’iyyar ADP ce kaɗai ta aika wa INEC da rahoton kuɗaɗen da ta kashe a zaɓen shugaban ƙasa.
ADP ta bayyana kuɗin a jimlace bayan dogon bayani cewa sun kai naira miliyan 95,388,417.
Sai dai kuma ADP ba ta haɗa da kwafen rantsuwar-kaffarar-kotu ba, kamar yadda INEC ta buƙata, wato affidavit.
Jam”iyyun da su ka karya wannan doka sun haɗa har da APC, PDP, APGA, AA, AAC, ADC, LP, PRP, da NNPP. Sauran sun haɗa da APM, APP, NRM, SDP, YPP da ZIP.
Sabuwar Dokar Adadin Kashe Kuɗaɗen Kamfen:
Yayin da INEC ta kasa hukunta yadda aka yi wa dokar kashe kuɗaɗen kamfen rugu-rugu a zaɓen 2019, yanzu kuma sai Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022 ta amince wa jam’iyyu cewa za su iya kashe har naira biliyan 5 a zaɓen shugaban ƙasa. Shi ma ɗan takarar gwamna aka yi masa ƙarin geji, daga naira miliyan 200 zuwa har naira biliyan 1.
An yi wa ɗan takarar sanata ƙarin geji daga naira miliyan 40, zuwa miliyan 200. Shi kuma ɗan takarar majalisar tarayya daga naira miliyan 10 zuwa naira miliyan 70.
PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Daraktan Bin Diddigin Kuɗaɗen Jam’iyyu na INEC, Aminu Idris, wanda ya tabbatar da cewa jam’iyyun duk sun karya dokar zaɓe a 2019.
Sai dai kuma ya kasa bayyana dalilin da ya sa INEC ta ƙi hukunta su.
Kakakin Yaɗa Labaran INEC, Festus Okoye shi ma cewa ya yi ba shi da masaniyar ko sun karya dokar, don haka a koma a tuntuɓi Aminu Idris.