‘Yan bindiga sun kashe mutum 16 a kauyuka jihar Zamfara

Mazauna garin Birnin Magaji dake jihar Zamfara sun koka cewa mahara ba za su daina kawo musu hari ba suna kashe mutane idan ba a cire jami’an tsaro da aka saka a garin ba.
PREMIUM TIMES ta tattauna da wasu mutane hudu daga kauyukan Birnin Magaji, Mazauda, Nasarawa Mai layi da Gidan Kane inda suka bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum 16 sannan wasu da dama sun ji rauni a lokacin da aka kawo wannan hari.
Mutanen da da aka tattauna da su sun ce maharan sun hana noma a yankin.
Wani mazaunin kauyen Gidan Kane ya ce ‘yan bindiga sun kashe mutane uku a wasu kauyuka a daren Lahadin da ya gabata.
“Maharan sun kashe mutum biyu a kauyen Tunkida, biyu a Mashayawo da wasu hudu a Mazauda. Maharan sun rika bi kauyuka suna kashe mutane.
“A ranar Litini maharan sun kashe mutum uku a kauyen Maituri da ke karkashin gundumar Gusami Hayi.
Mazaunin ya ce a ranar Lahadin maharan sun kai hari kauyen Tungar Danjima da Kiri Fada inda a kauyen suka kashe mutum hudu. Maharan sun afka wadannan kauyuka da rana tsaka dai dai an idar da sallah.
“Mahara sun ci gaba da kai wa mutane hari a yankin a cikin kwanakin da suka gabata. Misali a cikin kwanakin biyu da suka gabata maharan sun kai hari a kauyukan dake Mazauda, Tunkuda, Tungar Danjuma, Mashayawo, Nasarawa Mai layi da Kiri-Fada.
Wani mazaunin kauyen Mazauda ya ce maharan sun shaida musu cewa baza su daina kawo musu hari ba idan har ba a cire jami’an tsaron dake yankin ba.
“Maharan sun ce za su ci gaba da kawo mana hari saboda Muna hada baki da sojoji da ‘yan banga suna halaka su. A wani zama da wasu manya daga kauyen mu suka yi da Fulani ‘yan bindiga maharan sun ce za su ci gaba da kawo mana hari tunda muna kiran sojoji idan suka zo.
Suma mazauna kauyen Gidan Kane sun ce maharan sun ce za su daina kawo musu hari ne idan aka cire jami’an tsaron dake yankin.