An gurfanar da wani mai shekaru 35 a gaban kotu bisa laifin yi wa ‘yar shekara 2 Fyade

Kotun majistare dake sauraren kararrakin cin zarafin mata da yara kanana dake Awka, jihar Anambra ta gurfanar da Joseph Egwuatu mai shekaru 35 bisa laifin yi wa ‘yar dan uwansu mai shekara biyu fyade.
Egwuatu ya kai wa dan uwana ziyara ya aiki ‘yar rainon dake tare da yarinyar inda kafin ta dawo ya yi maza ya danne yarinyar.
Wannan abin takaicin dai ya faru a kauyen Nzam dake karamar hukumar Anambra ta Yamma.
Bisa ga sanarwar da mai taimakawa kwamishinan harkokin mata na jihar kan harkokin yada labarai Chidinma Ikeanyiownu ta fitar ya nuna cewa an kai Egwuatu kotu ranar Laraba sannan kotun kama shi bisa laifin yi wa ‘yar shekara 2 fyade.
Ikeanyiownu ta ce alkalin kotun Genevieve Osakwe ta yi watsi da rokon sassauci da Egwuatu ya yi a dalilin cewa kotun ba ta ikon sauraren karar.
Da yake ganawa da menema labarai bayan an tashi kotun Egwuatu ya musanta laifin fyaden da ake zarginsa da shi.
Ya ce ko da ya ziyarci gidan dan uwansa ya iske yarinyar a hannun mai rainon ta inda ya karbeta domin ya taya mai rainon.
“Zuwa Wani lokaci sai na tashi na shiga daki na dauko wani abu inda kafin na fito sai na ji ihun yarinya. Ina fitowa sai na ganta kwance a kasa jini duk a gabanta.
Zuwa yanzu dai an kai yarinyar asibiti likitoci na duba ta.