YAJIN AIKIN ‘YAN ADAIDAITA A KANO: Gwamnati za ta musanya su da sabbin tsarin sufirin cikin gari

A dalilin yajin aikin da ‘yan a daidaita sahu suka yi a jihar Kano gwamnati Kano karkashin Gwamna Abdullahi Ganduje ta ce za ta shigo da sabbin tsarin sufuri a jihar.

Idan ba a manta a ranar Litini ne masu ‘yan adaidaita suka fara yajin aiki na tsawon kwanaki 7 a jihar saboda gwamnati ta tilasta musu yin rajista da biyan karin haraji.

Shugaban hukumar kula da zirga-zirgan ababen hawa na jihar Kano Baffa Babba-Dan’agundi ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai kan yajin aikin da masu masu keke suka fara a jihar da kuma irin matsalolin da mutane suka shiga.

Babba-Dan’agundi ya ce gwamnati za ta shigo da sabbir tsarin sufuri a jihar domin canza yanayin sufuri da rage wahalhalun da mutane suka shiga a dalilin rashin abin hawa.

Babba-Dan’agundi ya ce gwamnati ta saka wannan tsari na biyan haraji ne domin kama masu aikata miyagun aiyukka da suke boyewa da aikin Keke.

Ya ce gwamnati ta rage farashin harajin da masu keke za su biya zuwa Naira 8,000 daga 100,000.

“Wasu daga cikin su sun biya amma da dama daga cikinsu sun ki biya sannan duk da haka suka shiga yajin aiki.

Babba-Dan’agundi ya ce gwamnati za ta tallafa wa masu Keken da ‘yan daba suka lalata musu Keke a dalilin sun ki shiga yajin aikin.

Har yanzu dai mutanen jihar Kano suna dandana kudar su na rashin adaidaita wasu na yin tattaki mai tsawo kafin su kai inda suke.