Kaban ciki ba aljanu bane ko alamun shiken mutuwa zai mutu kenan – Inji Likita

A taron horas da jami’an asibiti kan cutar kaban ciki dake kama mata da aka yi a Warri jihar Delta likitan mata dake aiki a kasar Asutralia Uche Menakaya ya bayyana cewa kaban ciki ba matsala ce ta aljanu ba ko kuma alamun mutum zai mutu kenan.

Menakaya ya ce kaban ciki cuta ce dake kama mahaifar mace a dalilin wasu canjin sinadarin garkuwar jikin mace.

Cutar ta fi kama daga yankin Afrika da duk mace baka.

Ya ce ana iya gano wannan cuta ce ta hanyar yin gwaji wato daukan hoton cikin mace.

“Likitoci za su iya yi wa mace fida domin ciro kaban ko Kuma su ba mace magani ta sha domin kawar da shi.

“Ya danganta da girman kaban a cikin mace amma mata da dama na haihuwa da kaban ciki a cikinsu.

Menakaya ya ce ya shirya taron horas da jami’an lafiya game da yadda ake kula da masu fama da wannan cuta domin inganta kiwon lafiyan mata a Najeriya.

“Kafin na fara aiki a Australia mata da dama a Najeriya na ganin cewa kaban ciki aljanu ne suka shafi mutum ko Kuma alamu ne na mutuwa.

“Horon da muka yi wa jami’an lafiya shine amfani da na’urar gwaji ta zamani domin gano cutar a jikin mace a farkon zuwan mace asibiti.