Yajin aikin ma’aikatan kotuna ya tsayar da shari’ar Diezani cak

Yajin aikin da ‘yan Kungiyar Ma’aikatan Kotunan Najeriya (JUSUN) ke yi ya kawo tsaiko wajen ci gaba da gudanar da tuhumar da ake yi wa tsohuwar Ministar Fetur a zamanin Jonathan, wato Diezani Allison-Maduekwe a Babbar Kotun Tarayya, Abuja.

Tun da farko dai an kasa zaman shari’ar a cikin watan Afrilu, saboda yajin aiki. Tunanin hakan ya sa Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ta dage sauraren karar zuwa 17 Ga Mayu.

Sai dai kuma da ranar ta zo, kotun ta ci gaba da kasancewa a garkame, saboda yajin aikin da JUSUN ke ci gaba da yi a fadin kasar nan.

Shari’ar Diezani na daya daga cikin manya da kananan shari’un da su ka kakare saboda yajin aikin da ya hana bude dukkan kotuna.

Diezani wadda ta yi Ministar Fetur a zamanin gwamnatin
Jonathan, EFCC ta maka ta kotu bayan ta gudu zuwa kasar Ingila bayan saukar su daga mulki, cikin 2015.

Ana tuhumar ta da laifuka 12 wadanda su ka shafi harkalla da satar makudan kudade.

Daga cikin tuhume-tuhumen, akwai na satar dala miliyan 39.7 da ke a gaban Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu.

Kwanan nan kuma PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda aka kwato dala miliyan 153 da kadarori 80 a hannun Diezani.

Shugaban EFCC Abdulrashid Bawa ya bayyana cewa an samu nasarar kwato zunzurutun dala miliyan 153 da kuma kantama-kantama da kananan kadarori daga hannun tsohuwar Ministar Man Fetur, Diezani Alison-Madueke.

Bawa ya ce kadarorin da aka kwato daga hannun Diezani za su kai kiyasin kudi har dala miliyan 80.

Shugaban EFCC ya yi wannan bayani ne cikin wata tattaunawa da Mujallar ‘Alert’, wadda EFCC ke bugawa ta yi da shi ta watan Afrilu.

Ita ma tattaunawar, Alert ta tsakuro ta ne daga cikin wata tattaunawa da Gidan Talbijin na Kasa, NTA ya yi da Bawa.

Kafin nada shi shugabancin EFCC, Bawa ne shugaban rukunin jami’an EFCC masu binciken Diezani, abokan burmin harkallar ta da kuma kadarorin su.

Diezani ta kasance zaman gudun hijira a Landan tun bayan cikar wa’adin gwamnatin Goodluck Jonathan a Mayu, 2015.

Sai dai kuma duk da wadannan makudan kudade da ake zargin ta sata da tulin kadarori, dawo da Diezani gida Najeriya domin a hukunta ta ya zama jan aiki ga EFCC da Gwamnatin Tarayya.

“Kun san akwai harkalloli masu yawa a kan Diezani. Da ni aka rika gudanar da binciken ta. A harkalla daya mun kwato dala miliyan 153, sannan mun samu izni daga kotu mun kwato kadarori 80 duk na Diezani, wadanda kiyasin kudin su sun kai dala miliyan 80.” Inji Bawa.

“Sai kuma batun harkallar da kafafen yada labarai su ka makala wa suna ‘toshiyar bakin INEC’ ta dala miliyan 115. Ita ma ana kan bincike a fadin kasar nan.

“Har yanzu ana kan binciken ta. Kawai abin da mu ke so shi ne a samu nasarar maido ta gida har mu gurfanar da ita.’

Ko a ranar Litinin ta 17 Ga Mayu, za a ci gaba da sauraren karar ta. Sai dai kuma zai yi wahala kotu ta zauna s narar, saboda har yanzu ma’aikatan kotuna su na yajin aiki.

“Ina tabbatar maku babu yadda za a yi wani jami’in EFCC ya kwato kadara sannan ya rika amfani da ita, ko ya bayar da hayar ta kuma ya sa kudin aljihu.”