Yadda rubabbun ma’aikatan Asibiti suka rika dankara min allurai, na rasa da na, na rasa mahaifa ta – Rukayya Abubakar

Wata matar aure maisuna Rukaya Abubakar mai shekara 25 ta koka da yadda rashin mai da hankali a aiki da jami’an lafiya na asibitin PHC dake Daddere a jihar Nasarawa ya sa ta rasa mahaifar ta.

Rukaya ta bayyana cewa tana da burin ta haihu ‘ya’ya 8 da mijinta amma sai hakan bai tabbata ba bayan ta haihu biyar.

Ta ce a Janairun 2023 bayan ta fara nakudar haihuwa ne mijinta ya kaita asibitin Daddere dake da nisan kilomita daya daga gidan ta domin ta haihu.

“Shigar mu asibitin ke da wuya sai nas ta rika mun allurai inda nakudan ya dawo Sabo.

“Ina cikin wannan hali ne na ce mijina ya kai ni wani asibitin kada in mutu.

“Zuwa can sai jami’an asibitin suka ce mu je asibitin Dalhatu domin su duba ni.

“Bayan sun duba ni a asibitin Dalhatu sai jami’an lafiya suka bayyana wa mijina da ‘yan uwa na cewa dole ayi mun fida saboda mahaifa na ya lalace kuma dan dake cikina ya mutu. Sun kuma tabbatar cewa idan har ba a yi mun fida ba zan iya shekawa lahira.

“A nan ne na tabbatar cewa jami’an asibitin Daddere sun illata ne, a dalilin wannan allurai da suka rika dirka min a lokacin da na ce asibitin.

Rukaya ta ce ta yi kwanaki 7 a asibitin tana jinya sannan ta dawo gida babu da babu mahaifa.

Wata Zainab Bashir ta ce ta gwamace ta haihu a gida saboda rashin kwararrun ma’aikatan lafiya a asibitin PHC Daddere.

“Haihuwa na hudu kuma na haife su duka a gida lafiya.

Jihar Nasarawa na daga cikin jihohin Najeriya dake yawan saman mace-macen yara kanana da mata wajen haihuwa.

Sakamakon binciken da Babban Bankin Duniya yayi a shekarar 2017 ya nuna cewa a duk shekara mata 700 daga cikin 10,000 ne ke mutuwa duk sannan jarirai 103 cikin jarirai 1,000 da ake haihuwa ke rasuwa duk Najeriya.

Asibitin PHC Daddere

Shugaban asibitin PHC Daddere Hassana Osabo ta bayyana cewa asibitin su ba su yi wa Rukaya allurai ba saboda asibitin na sane da wasu matsaloli da Rukaya ta samu a cikin da ta yi kafin wannan ciki.

Osabo ta ce Ungoxoma a asibitin ne suka fara duba Rukaya a lokacin da suka zo asibiti sannan ita daga baya ta zo asibitin.

“Bayan da muka duba ta ne muka aika da su asibitin Dalhatu domin kwararrun likitoci su duba ta.

Bayan haka Osabo ta ce a lokacin da Rukaya take zuwa asibitin yin awo, gwaji ya nuna cewa dan dake cikin Rukaya ya yi girma da yawa sannan akwai alamun cewa Rukaya ba za ta iya haihuwa da kanta ba.

Ta ce a dalilin haka ya sa muka aika da su asibitin Dalhatu dake Lafia.