Yadda na tsara cigaban Jigawa ta fannin fasahar sadarwa ta zamani – Danmodi

Dan takarar gwamna na Jam’iyyar APC a Jigawa, Umar Namadi, wadda akafi saninsa da ‘Danmodi’ ya ce idan aka zabe shi a matsayin gwamna zai bayar da muhimmanci kan fannin bayanai da fasahar sadarwa ta zamani (ICT) domin samun cigaban tattalin arziki da na zamantakewa a Jigawa.
Umar wadda ya bayyana hakan a cikin kundi na musanman mai bayyana manufofinsa na cigaban Jihar Jigawa.
Yace zai samar da yanayin da zai wanzar da hada-hadar ayyukan fasahar sadarwa ta zamani a Jihar ta hanyar samar da dokoki da tsare-tsaren gudanarwa na fannin.
Za mu zuba kuɗaɗe don samar da kayayyakin fasahar sadarwa da na’ura mai ƙwaƙwalwa, inda za mu faɗaɗa damar samun sadarwar intanet a faɗin jihad, cewar dan takarar gwamnar.
Ya kara da cewa domin ɗora Jigawa a turbar tattalin arziki da ya ginu kan ilimi tare da mayar da hankali wajen gina tattalin arziki mai fasahar zamani wanda zai ta’allaƙa musamman kan aiki da basirar na’ura (Artificial Intelligence) da kuma kimiyyar sarrafa bayanai (Data Science).
“Za mu samar da hanyoyin magance matsaloli kamar: ƙarancin kayayyaki da ayyukan fasahar na’ura, rashin daidaito a harkokin mulki, ƙaruwar tazarar bambanci tsakanin masu ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa da marasa shi, ƙarancin harkokin bincike da ƙirƙira a al’amuran gwamnati, kasuwanci tare da samun dama da ƙwarewa a fannin ƙirƙira, gami da koma-baya wajen karɓar sabuwar fasahar sadarwa ta zamani.
“Za mu yi amfani da cibiyar aikin kwamfuta da fasahar sadarwa da ke Hasumayar Galaxy a birnin Dutse da kuma wasu cibiyoyi bakwai (7) da hukumar NITDA ta samar a faɗin jihar, gami da sauran wuraren harkokin kwamfuta da fasahar sadarwa masu zaman kansu domin aiwatar da wannan tsari.
“Za mu hanzarta aiwatar da aiki da fasahar na’ura da sadarwar zamani domin ƙirƙira da kuma gano sababbin damarmaki a cikin jiharmu. Wannan zai buɗe mana hanyoyin tattalin arziki a zamanance domin samun bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa wanda ya shafi kowa da kowa.
“Za mu yi ƙoƙarin jawo masu zuba hannun jari a fannin tattalin arziki mai fasahar zamani domin maido wa Jigawa da matsayinta na jagora a harkar ICT. A nan za mu maida hankali wajen dauwamar da aiki da fasahar na’ura domin samun cigaba da ya haɗa da kowane ɗan jiha, faɗaɗa ayyukan bincike da ƙirƙira ta hanyar yin amfani da kayayyakin fasahar zamani.
“Wannan manufa za ta haifar mana da hanyoyi biyu wajen gaggauta aiwatar da al’amuran fasahar zamani da ƙirƙira: za ta bunƙasa sadarwar fasahar na’ura don samun cigaban da ya shafi kowa da kuma daidaita tsarin bincike da ƙirƙira domin inganta harkar kasuwanci, samar da hanyoyin samu, da bunƙasar tattalin arziki.
“Za mu tabbatar da an dauwamar da aiki da fasahar sadarwa a aikin gwamnati. Za mu samar da dandazon ƙwararru a fannin fasahar na’ura da sadarwar zamani a jiharmu, inji Malam Umar.