QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

Wasannin da aka buga na biyu a ranakun 28 da 29 ga Nuwamba, ya nuna yadda ƙungiyoyin Afrika uku su ka yi ƙoƙarin ganin sun kai ga tsakkakawa zagaye na biyu ɗin gasar.

Morocco wadda a wasan farko ta buga kunnen-doki, a yanzu ta na da maki 4 a Rukunin F. Dukan tsiyan da ta yi wa Belgium ya sa Morocco ta samu ƙwarin guiwar iya kaiwa zagaye na biyu, matsawar dai ta samu ba ta sha kashi a wasan ta na gaba ba.

A Rukunin H har yanzu a wasa biyu Kamaru na da maki 1 kacal. Wasan da su ka buga 3:3 ita da Sabiya ya nuna da wahalar gaske Kamaru ta iya fitowa daga daga rukunin ta.

Sai dai kuma ɗan wasan ta ya kafa tarihi. Aboubakar ya zama ɗan wasan da ya fara cin ƙwallo bayan ya shigo ya canji wani ɗan wasan.

Nasarar da Ghana ta yi kan Koriya ta Arewa, ya sa ƙasar na iya kaiwa ga zagaye na biyu, amma idan ta yi ƙoƙari kamar yadda ta yi a wasan ta da Koriya ta Arewa.

Senegal ita ma ta na da maki uku, kuma ta na kan siraɗi, kamar yadda ita ma Tunisiya mai maki ɗaya tal.

Akwai jan aiki a gaban ƙungiyoyin Afrika, musamman ganin cewa zai yi wahala su fara jin ƙamshin Kofin Duniya, saboda dalilai da dama.

Fitaccen mai horas da ƙwallon ƙafa Jose Mourinho ya taɓa cewa matuƙar ‘yan asalin Afrika na tsallakawa su na buga wa ƙasashen Turai wasa, to zai yi wahala wata ƙasa daga nahiyar ta lashe kofin duniya.

Ya ce idan da za a hana ‘yan Afrika buga wa wata ƙasar, to babu shakka ba da daɗewa ba wata ƙasa a Afrika za ta kafa tarihin lashe zaɓen Kofin Duniya.

Ƙasashen da su ka je QATAR 2022 tare da ‘yan Afrika a cikin ƙungiyar su, sun haɗa da Jamus, Ingila da wasu ƙasashen da dama.