Yadda jami’an harƙalla a Hukumar CCB ke kai wa ma’aikacin da ya mutu albashin sa har cikin kabari

Majalisar Dattawa ta gano yadda aka ɗirka harƙallar kwangilar sayen kayan aiki da su ka haɗa da firji, taroyin mota, takardu da sauran su na naira miliyan 995 a Hukumar Ladabta Ma’aikata (CCB).

Badaƙalar wadda aka ɗirka cikin 2015, Ofishin Akanta Janar na Tarayya ne ya bankaɗo ta, kuma ya aika wa Majalisar Dattawa a cikin watan Yuni.

An kuma gano cewa babu wata rubutacciyar shaidar rasiɗi ko wata hujjar cewa an sayi kayan.

Bayan wannan kuma, an bankaɗo yadda aka riƙa biyan wasu ma’aikata albashi har tsawon watanni shida bayan mutuwar ɗaya, shi kuma ɗayan aka riƙa biyan sa watanni hudu bayan ya yi ritaya.

Jami’an dai ba a bayyana sunayen su ba. Amma dai mamacin ‘ya riƙa karɓar albashi’ na naira 128,714, tsawon watanni shida bayan mutuwar sa.

Adadin kuɗaɗen da ya karɓa sun kai naira 772,289.

Shi kuma wanda ya yi ritaya an biya shi albashin naira 242,275 a kowane wata har tsawon watanni huɗu, daidai naira 971,061.

Yayin da Akanta Janar ya umarci Majalisa ta tilasta jami’in da ya biya albashin matacce cewa ya biya kuɗaɗen, kuma a hukunta shi. A cire kuɗaɗen daga Asusun Fansho na wanda ya biya mamaci albashin.

A ɓangaren wanda ya yi ritaya kuwa cewa Ajalinta ya yi a cire kuɗaɗen daga Asusun Fansho na wanda ya yi ritayar, kuma a hukunta jami’in da ya biya shi kudin.

Haka kuma Akanta Janar ya nemi a aika wa ofishin sa takardun shaidun an biya kudaden kuma an hukunta waɗanda su ka aikata laifin.