Gwamna Bagudu yayi alhinin kashe sojoji 7 da ƴan bindiga suka yi a Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu yayi alhinin kisan sojoji 7 da ƴan bindiga suka yi a Marke.

Gwamnan yayi tattaki har zuwa asibitin da ake duba sojojin dake jinya a asibitin.

Sai dai rahotanni sun ce jar yanzu ba a ga wasu sojoji biyu da suka ɓace a lokacin da suke gumirzu da ƴan bindiga.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda wasu ƴan bindiga suka kaiwa wasu sojoji harin kwantan ɓauna, suka kashe soja 7, 5 kuma suka ji rauni.

Kamar yadda muka jiwo daga majiyar mu ta sirri, sai da aka yi bata kashi tsakanin sojojin da ƴan bindiga amma da yake sun fi su yawa sun yi nasara akan sojojin Najeriya.

Sannan kuma sun kwashi bindigogin sojojin Najeriya.

Rashin tsaro yayi tsanani a Yankin Arewa Yamma yanzu inda kusan jihohin yankin gaba ɗaya ke cikin tsananin rashin zaman lafiya.