Yadda aka ceto ƴan matan Zamfara huɗu, bayan sun shafe watanni bakwai cur a hannun ‘yan bindiga

A ranar Alhamis ce Gwamnatin Jihar Zamfara ta karɓi ‘yan mata huɗu da su ka shafe watanni bakwai a hannun ‘yan bindiga.
An kai su Gidan Gwamnatin Zamfara ne bayan ‘yan bindigar sun sake su.
‘Yan matan da su ka haɗa Jamila Isa, A’isha Isa, Ummulkahairi Musa da Ummulkhairi Umar, an yi garkuwa da su ne lokacin da su ke kan hanyar zuwa Birnin Magaji daga Kaura Namoda.
Kama daga gwamnatin jihar da kuma iyayen ‘yan matan, na wanda ya furta cewa sai da aka biya kuɗin fansa kafin a sako su.
Sai dai wannan jarida ta samu tabbacin cewa wasu jami’an SSS ne su ka kai su Gidan Gwamnatin Zamfara, domin su gana da Gwamna.
Cikin sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Idris ya fitar, ya ce “gwamnatin jihar ce ta shiga ta fita, har aka saki ‘yan matan.”
Ya ce Gwamnatin Zamfara ta damu ƙwarai ganin yadda aka nuna wani bidiyo, inda a ciki aka ga yadda yaran ke ke kuka a cikin alhini, su na roƙon iyayen su da Gwamnatin Zamfara ta cece su.
“A matsayi na na Gwamnan Jihar Zamfara, ina so na nuna godiya ta ga Allah da ya kuɓutar da yaran nan, waɗanda aka yi garkuwa da su tsawon watanni bakwai.
“Lallai wannan lokaci ne na farin ciki ga gwamnati da iyalan su. Ina kira ga waɗannan yara da su ka kuɓuta cewa su ɗauki abin da ya faru da su a matsayin ƙaddara ce daga Allah Maɗaukaki. Kada abin da ya same su ya dugunzuma su, har ya shafi rayuwar su.
Haka Dauda Lawal ya bayyana, ta bakwai Kakakin Yaɗa Labaran sa.
Gwamnan ya ce za a kula da ‘yan matan su huɗu ta yadda za a saisaita rayuwar su a cikin al’umma.
Yayin da PREMIUM TIMES ta tuntuɓi ɗaya daga cikin kawun wata yarinyar, wadda ‘yar asalin ƙauyen Kura ce daga Ƙaramar Hukumar Bunguɗu, cewa ya yi:
“Ni ba zan ce komai ba. Mu na farin ciki da kuɓutar yaran. Abin da ke gaban mu a yanzu shi ne dawowar da su ka yi da ran su. Ku kuma ‘yan jarida mun gode dangane da yadda ku ka watsa irin matsanancin halin da yaran su ke ciki a hannun ‘yan bindiga, har aka shiga aka fita, aka kuɓutar da su.”