Yadda ƙoƙarin ɗinke ɓarakar PDP ya kai Wabara kujerar Shugaban Kwamitin Dattawan jam’iyya

Jam’iyyar PDP ta zaɓi tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Adolphus Wabara zama Shugaban Riƙo na Kwamitin Amintattun, bayan murabus ɗin da shugaban kwamitin Walid Jibrin ya yi a ranar Alhamis.
Walid Jibrin ya ce ya sauka ne domin ya bayar da sararin yadda ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar zai yi gagarimar nasara a zaɓen 2022.
Shugaban PDP Iyorchia Ayu ne ya bayar da sanarwar saukar Wabara a lokacin da su ka zauna Taron Majalisar Zartaswa ta PDP (NEC), jim kaɗan bayan kammala Taron Kwamitin Dattawan PDP ɗin.
“To a yau dai Shugaban Kwamitin Dattawa Walid Jibrin ya sauka daga muƙamin sa, bayan ya yi wa jam’iyyar mu ƙasaitaccen aiki. Mu na gode masa ƙwarai.” Inji Ayu.
Wanda aka naɗa riƙon ƙwarya dai ɗan asalin Jihar Abiya ne, kuma kafin naɗa shi, shi ne Sakataren Kwamitin Dattawan.
Shi kan sa Ayu ya na fuskantar matsin lambar ya sauka daga ɓangaren Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas da magoya bayan sa.