Wata masarauta a Neja ta gargaɗi basaraken ta ya daina kwalliya ɗaya da Sarki

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Masarautar Bida dake jihar Neja ta umarci Basarakenta Alhaji Abubakar Wachin, Hakimin Kutigi (Ezanuwan Kutigi) da ya daina kwalliya da Alkyabba biyu kamar Sarki domin shigar bata dace da sarautarsa ba.

Umarnin masarautar na cikin wata dakarda da Hausa Daily Times ta samu ɗauke da sa hannun Magatakardan Masarautar Malam Abdulmalik Usman (Nagyan Nupe). Tana mai cewa basaraken ya karbi gaisuwa a matsayin “Zaki” kamar yadda dukkan Hakiman Ƙauyukan masarautar ke amsawa, tare da umartarsa da ya daina amsar gaisuwar “Bagadozhi” domin wannan Sarki ne kawai ya cancaci ya karbeta.

Takardar ta ce sarautar Ezanuwan daidai take da sarautar Zanna da yaren Kanuri, dan haka gaisuwarsa ba Bagadozhi bane. Dan haka masarautar ta ce ta tuntubi masarautar Kanuri ta Borno kuma ta gano cewa “Alangubro” da yaren Kanuri ko kuma “Barata Barata” shine gaisuwar da ta dace da duk mai sarautar irin na Ezanuwa, inda shi kuwa zai amsa da “Baraninmin Baraninmin” da yaren Kanuri kenan.

Masarautar Bida dai ita ce ta ɗaya a jerin manyan masarautu 8 dake jihar kuma Sarkin Bida, Mai Martaba Manjo Janar Yahaya Abubakar (mai ritaya) shi ne yake jagorantar majalisar Sarakunan jihar.

Ko a kwanakin baya an samu makamancin haka a jihar Bauchi tsakanin Masarautar Bauchi da Wakilin Birnin Bauchi bisa gasar kwalliya da Sarkin Bauchi a taruka da dama wanda hakan ya sa masarautar ta dakatar da shi, a cewarta, ta sha yi masa gargaɗi amma ya ƙi ji.