TUBAN MUZURU: Ƴan Bindiga sun harbe Auwalun Daudawa

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Tashar Radiyo na DW ta ruwaito mutuwar Tubabben jagoran ƴan bindigan nan Auwalu Daudawa da ya jagoranci sace ɗaliban sakandaren Ƙanƙara ta jihar Katsina.

Tashar ta ce Kwamishina harkokin cikin gida da tsaro na jihar Zamfara Abubakar Justice Dauran ya tabbatar mata da aukuwar wannan lamari.

Ta ce Kwamishinan ya ce sun samu labarin Auwalu Daudawa ya sake komawa daji domin ci gaba da aikata ta’addanci bayan ya tuba wanda a nan ne aka yi ajalinsa.

Abubakar Justice Dauran ya ce Daudawa ya sanar da su cewa ya tafi Daji bikin ƴan uwansa ashe basu sani ba daji ya koma, a nan ne ya kora garken Shanayen wasu Fulani ƴan uwansu su kuwa suka harbeshi har lahira.