Yadda na shafe kwanaki 25 a hannun Fulanin da su ka yi garkuwa da ni – Wazirin Dansadau

Alhaji Mustaoha Umar shi ne Wazirin Dansadau, garin da ke cikin Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

A zantawar sa da PREMIUM TIMES HAUSA, ya bada labarin irin bakar wahala da dukan da ya ci a hannun masu garkuwa, wadanda su ka tsare shi tsawon kwanaki 25, har sai da aka biya naira miliyan 4 sannan aka sako shi.

“Ni da kani na Isa Umar da wani mai suna Tukur Maigari, mun shiga hannun ‘yan bindiga a ranar 1 Ga Afrilu, bayan sun tare mu sun kama mu kuda da garin Dansadau, tazarar kilomita hudu.

“Mu na kan babura su ka tare mu. Kuma na fahimci kamar dakon mu su ka rika yi, har su ka cim mana. Wajen karfe 3 na yamma su ka kama mu. Daga nan su ks caje aljifan mu, kuma daure mana fuska, sannan su ka nausa da mu cikin daji.

“Sun rika yi mana tambayoyi, amma na yi masu karya na ce ni malamin firamare ne. Sai da su ka kai mu wani sansanin su inda su ka ajiye mu tsawon kwanaki uku. A can ne wani ya gane ni ne dillalin shanu kuma mai motar daukar shanu a Dansadau.

“Bayan mun shafe kwanaki uku, sai su ka kara nausawa da mu cikin daji, inda iyalan su da ‘ya’yan su kanana. A can mu ka shafe makonni uku kafin a biya kudin fansar mu.”

Waziri ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa matsalar garkuwa da mutane ba za ta gushe ba, har sai gwamnati ta yi da gaske ba.

Yadda Na Ci Dukan Tsiya A Hannun Masu Garkuwa:

“Sun ajiye mu cikin wata karamar bukka, su ka hana mu yin komai. Ko Sallah ma su ka ce ba za mu yi ba. Ko magana ma hana mu su ka yi. Idan ka ga mun yi magana, to an kira ne daga gida mu na tattauna cinikin biyan diyya.

“A kan jibge ni idan na kuskura na yi magana da Turanci ga wanda ya kira ta waya. To daga baya na nuna lallai sai na rika yin sallah.shi ne har aka rika debo min ruwan alwala.

“Mu na can tsare su ka kamo wasu mutum biyar su ka cusa mana su a cikin mu. Ga kuma bukkar karama ce, ko tsayuwar sallah ba za a iya yi a cikin ta ba.

“Ya’yan su kanana da ba su wuce shekaru 10 ba ake aikowa su na kawo mana abinci da safe, wani lokaci har da dare.

“Ranar da ‘yan bijilante su ka kashe Fulani a Dansadau, sun yi mana dukan tsiya saboda haushin an kashe dangin su.

“Amma da su ka kai hari a Magami ta Karamar Hukumar Gusau, sun dawo sun ce ba za su sake dukan mu ba, domin sun dauki fansa, wato sun kashe ‘yan bijilante da dama a Magami.

Bama-baman Da Sojoji Ke Jefawa Ba Ya Kashe Masu Garkuwa:

Waziri Mustapha ya kara da cewa ya fahimci hare-haren bama-bamai ba ya samun ‘yan bindiga, sai dai wadanda ba su da laifi.

“Wato da sun ji rugugin jirgin yaki, sai su kwashe bindigogi da iyalan su, su boye a karkashin inuwar mangwaro, ko wani wuri. Kuma duk sun san sunayen jiragen yaki. Sun san wanda ke zuwa shawagi kawai ya koma. “Mai Shulo” su ke kiran jirgin da ke jefa masu bama-bamai.

“Kuma jirgi ya jefa bam ya koma, sai Fulanin da yaran su kanana su rika tsalle su na murna, su na kuwwa, saboda ko kaza bam din bai kashe masu ba.”

Mustspha Umar ya ce ba a sake su ba sai da aka biya naira miliyan hudu, bayan sun shafe kwanaki 25.

Ya ce kafin a sake su, sai da ‘yan bindigar nan su ka lissafa kudin kaf, su ka tabbatar sun cika cif-cif.