Tsohon hadimin Buhari, Sharada ya fice daga jam’iyyar APC, ya koma ADP

Tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda yayi fice wajen kare shugaban kasa a musamman Arewacin Najeriya kuma dan asalin jihar Kano, Shaaban Ibrahim Sharada ya fice daga jam’iyyar APC.
Mai taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman kan Harkokin sadarwa na zamani, Bashir Ahmad ya tabbatar da haka a shafin sa na Facebook in da ya ce ” Yanzu nake samun labarin ficewar abokina kuma dan uwana Hon. Shaaban Ibrahim Sharada daga jam’iyyar mu ta APC zuwa African Democratic Party (ADP) wanda a yanzu ya samu tikitin jam’iyyar na takarar Gwamna a jihar Kano.
” Duk idan Shaaban Sharada ya samu kan sa a siyasance ko a mu’amalance zan kasance me yi masa fatan alheri da fatan samun nasara a rayuwarsa. Allah ya sa hakan ne mafi alheri a siyasar sa. Allah ya ci gaba da daukaka jihar mu, Kano da Nigeria baki daya.”
Idan ba a manta ba Sharada ya kalubalanci sakamakon zaben fidda gwani na jam’iyyar APC na gwamnan jihar, inda ya yace an tafka magudi a zaben da ta tsaida mataimakin gwamna umar Gawuna dan takarar gwamnan jihar.
Shima Sharada ya yi takarar gwamnan amma bai yi nasara ba.
Sharada ya koma jam’iyyar ADC kuma tuni har ya zama dan takarar gwamnan Kano a inuwar jam’iyyar.
Ba Sharada ba kawai, wasu daga cikin makusantan shuagaban kasa Muhammadu Buhari, da ya hada da Dan uwansa Fatahu dake wakiltar shiyyar Daura a majalisar Wakilai ta tarayya da sanatan yankin duk sun fice daga jam’iyyar APC.