A cikin shekara biyar Najeriya ta rage yawan mata da ake wa auren wuri – Rahoton

Rahoton da hukumar NICS ta gabatar ya nuna cewa a cikin shekara biyar Najeriya ta rage yawan mata da ake wa aure kafin su cika shekaru 18.

Rahoton ya nuna cewa Najeriya ta samu ragin kashi 30% a shekarar 2021 daga kashi 44% a shekarar 2016.

An gabatar da sakamakon gwajin a taron da NICS, MICS da UNICEF suka shirya.

Rahoton da NICS ya nuna Najeriya ta rage yawan mace-macen yara kananan daga mutuwan yaro daga daga cikin yara takwas a shekaran 2016 zuwa mutuwan yaro daya a cikin yara goma.

Daga nan kuma rahoton bada bayanan samun karuwar yadda mata ke shayar da ‘ya’yan su nonon uwa zalla daga kashi 24% zuwa 34% sannan da Karin yawan yaran da ake wa rajista a asibiti daga Kashi 47% zuwa 60%

Da yake tofa albarkacin bakinsa a taron Mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo wanda ministan kudi Zainab Ahmed ta wakilta ya ce sakamakon bincike irin haka na taimaka wa gwamnati wajen inganta yi wa yara kanana allurar rigakafi.

Zainab ta ce gwamnati za ta tsaro matakai da za su ingata tattalin arzikin kasa domin samun ci gaba a Najeriya.

Shugaban hukumar NBS Adeyemi Adeniran ya ce sakamakon binciken da NICS da MICS suka gabatar zai taimaka wajen inganta kiwon lafiyar yara kanana da mata a kasar nan.

Yankin Arewa na baya wajen yi wa yara allurar rigakafi

Zainab ta koka da yadda Arewa take baya wajen yi wa yara allurar rigakafi.

Ministar ta yi kira ga iyaye da gwamnatocin yankin su maida hankali akan aikin.