TONON SILILIN TASHOSHIN JIRAGEN RUWA: Yadda kwangilolin biliyoyin nairori su ka hada Amaechi da Hadiza Bala kakudubar rikici

Ashe dai kwatagwangwamar rikicin kwangilolin biliyoyin nairori ne su ka hada dakatacciyar Shugabar Hukumar Tashoshin Ruwa Hadiza Bala rikici ita da ogan ta, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.

Wasu gangariyar kwafen takardun da PREMIUM TIMES HAUSA ta damke a matsayin hujja, sun nuna cewa watanni kadan kafin dakatar da Hadiza a makon da ya gabata, ta tafka kadabolon rikici ita da Amaechi, kan wata gawurtacciyar kwangila.

Kakudubar rigima ta harde a tsakanin su, har sai da ta kai Ofishin Tantance Hakikanin Farashin Kwangila (BPP), Ministan Shari’a Abubakar Malami da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari duk sun sa baki a rigimar.

Gambari ya aika wa Amaechi da Hadiza da umarni daga Shugaba Muhammadu Buhari, kuma ya nemi shawara daga waje, domin sasanta lamarin.

Hadiza wadda aka dakatar da ita tare da Minista Amaechi ya yi ikirarin cewa ta kasa cike gibin naira biliyan 165 da su ka kamata ta zuba asusun Gwamnatin Tarayya, ta maida raddin cewa lissafin da Amaechi ya dogara da shi, lissafi ne amma na dawakan-Rano.

Gurungunduma Da Kwatagwangwamar Kwangilar Da Ta Hada Amaechi da Hadiza Bala Zare Wa Juna Idanu:

Dalla-dallar abin da PREMIUM TIMES HAUSA ta gani da idon ta, wato akwai wata narkekiyar kwangila wadda NPA ta rubuta wa Hukumar Tantance Tantagaryar Adadin Kudaden Kwangila (Bureau of Public Procurement, wato BPP), inda ta nemi a zabi kamfani daga cikin wasu kamfanoni 9 da su ka nemi kwangilar aikin yashe gaba da gangar bakin mashigar jiragen ruwa a gefen teku a Lagos. Bonny, Warri da Gundumar Excravos.

PREMIUM TIMES HAUSA ta gano cewa kudaden wannan kwangila sun kai naira biliyan 65. Kwangilar yasar rairayi da dagwalon kwatamin gefen tekun Lagos ta kai naira biliyan 31. Ita kuma kwangilar yasar rairayi da dagwalon kwatami a Tashar Ruwa ta Bonny, ta kai naira biliyan 34.

NPA ta ce ta nemi bin tsarin zaben kamfanin da ya dace ya yi aikin, saboda yanayin irin aikin. Sannan kuma kwangilar aikin hada-ka da ake yi tsakanin Kamfanin Kula da Yasar Yashi na Lagos, LPCMC da na Bonny, wato BCN, duk wa’adin cikar aikin su ya kare cikin Disamba, 2019 da kuma Yuni 2020.

Hukumar Tantance Tantagaryar Adadin Farashin Kudaden Kwangila, BPP ta amince da tsarin da NPA ta ce a bi wajen bayar da kwangilar.

Katsalandan Daga Amaechi:

Amincewar ke da wuya sai Amaechi ya ce bai yarda da tsarin da aka bi ba, kuma nan take ya soke kwangilar, sannan ya ce kamfanin da ke kan kwangilar wadda wa’adin ta ya cika, to a kara masa wa’adin shekara daya.

Amaechi ya ce ya yi haka ne bisa shawarar da ya ce BPP ta Hukumomin Gwamnati sun bayar, bisa dalili na barkewar cutar korona.

Ita kuma Hadiza ta rubuta a cikin wani bayani cewa Minista Amaechi ya yi korafin cewa an maida shi saniyar-ware wajen tsara bayar da kwangilar, kuma ya nuna damuwa dangane da zunzurutun kudaden da aka ware don biyan kwangilolin.

Sannan kuma Hadiza ta ce kamfanonin da Amaechi ya ce a kara wa wa’adin shekara daya, sun shafe shekaru 15 su na wannan aiki. Ga shi kuma wa’adin su ya kare a Agusta.

Sannan kuma Hadiza ta ce babu wani dalili da Minista Amaechi zai kafa hujja da cutar korona domin dukkan aikin tantance kwangilolin ta sakon kar-ta-kwana na tsarin aiken ‘courrier’ aka yi shi.

Daga nan sai ta ce idan Amaechi bai gamsu da kwangilar ba, zai iya umartar NPA a ka’idance ta soke kwangilar sannan ta kara wa kamfanonin da wa’adin su ya kare shekara daya.

Cikin wata wasika a ranar 2 Ga Yuni, 2020, ana tsakiyar korona, Ma’aikatar Sufuri ta umarci NPA ta janye sanarwar neman kamfanonin da za a bai wa kwangilar aikin yashe rairayin.

Wani Daraktan Kula da Harkokin Shari’a da Barutuwan Koru na Ma’aikatar Sufuri, mai suna Pius Oteh ne ya sa wa takardar hannu.

Kuma ya umarci NPA ta kara wa kamfanonin da ke kan aikin yashe rairayi da dagwalon gefen teku wa’adin shekara daya.

Nan take NPA ta bi umarnin da Ma’aikatar Sufuri ta bayar.

“Mu Ke Da Ikon Soke Kwangila, Ba Ma’aikatar Sufuri Ba” -BPP

Ganin umarnin da Minista Amaechi ya bai wa NPA, sai Hukumar BPP ta rattaba cewa, “akwai fa ayyukan da cutar korona ba za ta hana aiwatar da su ba, kuma BPP din ce ke da iznin soke kwangiloli ba Ma’aikatar Sufuri a karkashin Amaechi ba.”

WASIKAR BPP Ga NPA: “Ba Ma’aikatar Sufuri ke da hakkin soke kwangila ba, hakkin Hukumar BPP ne. Maimakon a soke kwangila, a kara wa’adin watanni shida, yadda zai zamana an samu bin tsarin tallata masu sha’awar yin kwangila kamar yadda kasashen duniya su ka tsara cewa a rika bi.

“Amma idan Hukumar NPA na ganin cewa soke kwangilar shi ne mafi alheri ga kasar nan da daukacin jama’ar ta, to za ta iya dakatar da kwangilar.”

Hukumar NPA karkashin Hadiza Bala ta saki umarnin Minista Amaechi ta bi umarnin Hukumar BPP. Ta ci gaba da tallata neman ‘yan kwangilar da kamfanonin da za su shiga takarar neman aikin kwangilar, wato ‘bidding’ kenan a Turance.

Sai dai kuma ana cikin aikin tantance kamfanonin ne aka dakatar da Hadiza Bala daga shugabancin NPA, tare da kafa mata kwamitin bincike.

PREMIUM TIMES HAUSA ta gano cewa an samu sabani kuma tsakanin Amaechi da Hadiza Bala dangane da gaban-gabarar da Hadiza din ta yi ta soke ayyukan da Intels, kamfanin Atiku Abubakar ke yi a Tashoshin Jiragen Ruwa.

PREMIUM TIMES HAUSA ta gano cewa Minista Amaechi bai goyi bayan a kori Intels ba, amma Hadiza ba ta bi turba daya da ministan ba.