Tattalin arzikin Najeriya ya yi fukafikin tashi sama cikin watannin Afrilu zuwa Yuni -NBS

Tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kashi 5.01% bisa 100% a cikin watannin Afrilu, Mayu da Yuni na shekarar nan ta 2021.

Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ce ta bayyana haka a ranar Alhamis, a Abuja.

Ƙaruwar tattalin arzikin ya biyo bayan naƙasun da tattalin arzikin ya samu a cikin watannin Janairu zuwa Maris da Afrilu zuwa Yuni a shekarar 2020 da ta gabata.

Wannan naƙasun da tattalin arzikin ya samu a farkon 2020 ne ya haifar da matsin tattalin arziki, ƙuncin rayuwa da karyewar tattalin arzikin sakamakon ɓarkewar cutar korona.

Cutar korona ta tsaida komai kama daga ayyuka, kamfanoni da masana’antu na gida da na ƙasashen waje. Sannan kuma ƙasashen duniya sun kulle kan iyakokin su na ruwa, na sama da na ƙasa.

Sai dai kuma a ƙarshen 2020 tattalin arzikin Najeriya ya nemi fara farfaɗowa, biyo bayan fara ɗage takunkumin zirga-zirga da hada-hadar kasuwanci a ƙasa da duniya.

Daga nan kuma ƙarfin tattalin arzikin cikin gida ya bunƙasa da kashi 2.70% a cikin 2021, idan aka kwatanta da yadda a cikin 2020 ya ja baya da -2.18 a tsakiyar shekarar 2020.

Ƙididdiga ta nuna irin bunƙasar da fannin fetur ya samu a yanzu, idan aka kwatanta da lokacin ɓarkewar korona, lokacin da darajar gangar ɗanyen mai ta koma daidai da darajar ruwan aski, cikin 2020.

Haka nan sauran ɓangarorin da ba harkokin mai ba sun samu bunƙasa fiye da cikin 2020.

Fannonin da suka bunƙasa da ba na ɓangaren fetur ba, sun haɗa da cinikayya, sandarwa, yaɗa labarai, zirga-zirga da sufuri, harkokin lantarki, fannin noman kayan gonar sayarwa, kayan abincin da masana’antu ke sareafawa da kuma kayayyakin lemukan kwalba, na gwangwani da na kwali.