Farmakin da ƴan bindiga su ka kai NDA tsokana da cin fuska ne ga Sojojin Najeriya – Shugaban Hukumar NHRC

Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin Jama’a, Tony Ojukwu, ya bayyana ce farmakin tattakin da ‘yan bindiga su ka yi har cikin NDA A Kaduna kan sojoji, cin fuska ne da tsakana ga Rundunar Sojojin Najeriya

Ojukwu ya bayyana cewa harin barazana ce da cin fuska ga harkar tsaron Najeriya baki ɗaya.

Haka ya bayyana a cikin wata sanarwar da Jami’ar Yaɗa Labarai ta NHRC, Fatimah Mohammed ta fitar wa manema labarai a ranar Laraba.

Da ya ke bayyana sojoji a matsayin su ne alfaharin ƙasa baki ɗaya, Ojukwu ya ci gaba da cewa, “wannan farmakin da aka kai a cibiyar horas da sojoji wadda ta shahara a duniya, can a ke horas da ƙwararrun masu leƙen asiri, to abin takaici ne matuƙa, ba a taɓa zato ba, kuma abin yin tir ne.” Inji Ojukwu.

Sai ya ci gaba da cewa farmakin abin haushi ne, kuma kisa da arcewa da wani jami’in soja abin damuwa ne matuƙa, kuma keta alfarmar ‘yancin ɗan Adam ne.”

Ya yi kira ga sojoji su yi dukkan bakin ƙoƙarin ganin sun ceto wanda aka yi garkuwa da shi, kuma su kamo maharan a hukunta su.

Shugaban NHRC ya yi ta’aziyya da jimami ga iyalan Laftanar Wulah da Filai Laftanar Okoronkwo, waɗanda mahara su ka bindige a lokacin farmakin.

Ojukwu ya ce sun sayar da rayukan su da mafificiyar tsadar kare ƙasar su ta haihuwa.

Yayin da ya ki kira ga Gwamnatin Tarayya ta ƙara tsaurara matakan tsaro a cikin ƙasa, Ojukwu ya kuma koka akan yadda Jihar Kaduna ta zama dandazon ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa wannan hari da aka kai Cibiyar Horas da Hafsoshin Sojoji (NDA) a Kaduna, za ta zama sanadin zaburar da sojojin Najeriya domin su kakkaɓe mahara da ‘yan bindiga.