TARON GWAMNONIN APC DA BUHARI: Za a yi gangamin jam’iyya cikin watan Fabrairu, 2022

Bayan da Gwamnonin Jam’iyyar APC su ka gana da Shugaba Muhammadu Buhari, shugabannin jam’iyyar sun amince su shirya gangamin taro na ƙasa a cikin watan Fabrairu, 2022. Haka dai wani jami’i a cikin jam’iyyar ya tabbatar da haka.

Gwamna Mai Mala-Buni kuma Shugaban Rikon APC kuma Gwamnan Jihar Yobe ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, bayan sun fito daga ganawar da su ka yi da Shugaba Buhari a fadar sa, ranar Litinin a Abuja.

Cikin waɗanda su ka halarci ganawa da Buhari, akwai gwamnan Kebbi Atiku Bagudu, na Jigawa Badaru Abubakar. Badaru shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC.

Buni ya ce an amince a gudanar da taron gangamin jam’iyya cikin watan Fabrairu a lokacin da shugabannin su su ka halarci taro a ranar Lahadi.

Ya ƙara da cewa har yanzu dai ba a cimma matsayar ranar da za a yi taron ba. Amma dai an cimma shirya shi cikin Fabrairu, bayan an tuntuɓi manyan masu ruwa da tsakin cikin APC.

Buni wanda shugabancin sa ke shan suka musamman a cikin manyan APC, ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake yi cewa zai nemi ƙarin wa’adin ci gaba da shugabancin APC.

“Ni ba ni da aiki ne da har ko da yaushe zan ta neman ƙarin wa’adin shugabanci ko me? Akwai nauyin da ke kai na wato shugabancin al’ummar Jihar Yobe. To shi na ke so idan an yi gangami, an zaɓi sabbin shugabanni, ni ma sai na koma jiha ta, na ci gaba da ƙoƙarin sauke nauyin da ke kai na.”

An naɗa Buni shugabancin kwamitin tafiyar da APC na mutum 13, a cikin watan Yuni, 2020, bayan an wancakalar da shugabancin Adams Oshiomhole.