TAKARAR GWAMNAN KADUNA: Uba Sani ya mika fom din takara ga uwar jam’iyya

A yau Talata ne sanata Uba Sani ya mika fom din takarar gwamna da ya siya ga uwar jam’iyya a Abuja bayan ya cika.
Idan ba a manta ba a cikin waran Afrilu ne sanata Uba Sani ya siya fom ɗin rakarar gwamnan jihar Kaduna.
Sanatan wanda shine ke wakiltar Kaduna ta Tsakiya a majalisar Dattawa ya sami amincewar gwamnan jihar a cikin makon jiya inda aka umarci sauran ƴan takara su janye masa domin a samu haɗin kai da nasara a zabe mai zuwa.
Tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kaduna, Mohammed Sani Dattijo ya janye wa sanata Uba Sani.
Sakataren tsare-tsare na jam’iyyar Mohammed Argungu ne ya karbi fom din a hedikwatar jam’iyyar.
Bayan haka sanata Uba ya zanta da manema labarai inda ya shaida masu cewa abinda ya ke a gaban sa yanzu shine ya ɗora daga inda gwamna El-Rufai ya tsaya,
” Wannnan tafiya ce na al’umma da mutanen jihar Kaduna. Dole mu jinjina wa shugaban mu kuma jagoran mu, gwamna Nasir El-Rufa’i bisa karamci da goya mu da yayi sannan kuma da cigaba da rangaɗa wa mutanen Kaduna ayyuka na cigaba kamar yadda za mu gada daga shugaban mu El-Rufa’i.
Daruruwan magoya baya ne suka raka sanata Uba wajen mika fom ɗin a Abuja ranar Talata.