Soke shirin NYSC zai ƙara raba kan ‘yan Najeriya -Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III ya bayyana cewa rushe tsarin bautar ƙasa da wasu ke ƙoƙarin yi ba zai haifa wa ƙasar nan alheri ba.

Ya ce idan aka rushe tsarin NYSC, wanda aka fi sani da Shirin Yi Wa Ƙasa Hidima, hakan zai tsinke igiyar haɗin kai da juna a tsakanin ƙabilu da bangarorin ƙasar nan.

Ya yi wannan bayani na rashin nuna goyon bayan soke shirin ne a lokacin da wasu ‘yan NYSC da aka tura Jihar Sokoto su ka kai masa ziyara a fadar sa.

Sarkin Musulmi ya ce masu hanƙoro da haƙilon sai an soke tsarin NYSC ba su neman ƙasar nan da akheri.

Ya ƙara da cewa an ƙirƙiro shirin NYSC ne domin ƙara danƙon haɗin kan al’ummomin Najeriya da kuma ƙabilu daban-daban.

“Na ji wasu na nan su na ta ƙoƙarin ganin an soke tsarin NYSC. To ni dai ina ganin waɗanda ke neman ganin an rushe tsarin aikin bautar ƙasa, ba su ƙaunar ƙasar nan da alheri.” Inji shi.

Ya ce a yanzu ne ma aka fi buƙatar ƙarfafa shirin NYSC saboda a yanzu ɗin ne haɗin kan ƙasar nan ke fuskantar barazana.

Sarkin Musulmi ya shawarce su da su kiyaye kuma su mutunta ɗabi’u da al’adun jama’ar da su ka karbi baƙuncin su a jihar Sokoto.

Sannan kuma ya hore su da yin kaffa-kaffa, saboda akwai matsalar tsaro a jihar Sokoto.