An yi kira da a fara yin gwajin cutar daji a cibiyoyin kiwon lafiya dake kusa da mutane

Wasu kungiyoyin masu zaman kansu sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fara yin gwajin cutar daji a cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a kasar nan.

Kungiyar ‘First Ladies against Cancer (FLAC)’ wanda daya ce daga cikin kungiyoyin da suka yi wannan kira ta ce yin haka zai inganta yin gwajin cutar da wayar da kan mutane game da cutar musamman mazauna karkara.

Shugaban kungiyar FLAC kuma uwar gidan gwamnan jihar Neja Amina Bello ta ce yin gwajin cutar zai taimaka wajen gano cutar da wuri sannan da rage tsadar kudin magani.

Amina ta kara da cewa sama da kashi 75% na mazauna kasar nan na kashe makudan kudade wajen sama ma kansu lafiya idan ba su da shi.

Ta ce domin kawo karshen haka kungiyar na kokarin ganin gwamnati ta ware isassun kudade domin ganin masu fama da cutar daji sun samu kula da kuma samun magani cikin sauki a kasar nan.

Amina ta ce gwamnati ta yi alkawarin saka cutar daji a cikin inshoran lafiya.

Idan ba a manta ba a taron tattauna hanyoyin inganta kiwon lafiya da aka yi shekaran 2019 ministan lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa gwamnati za ta bude asusu domin tallafa wa masu fama da cutar daji a kasar nan.

Sai dai masu fama da cutar sun ce har yanzu basu fara samun tallafi daga gwamnati ba.

Shugaban kwamitin kiwon lafiya na majalisar tarayya, Tanko Sununu ya ce har yanzu gwamnati na kokarin tsaro matakan da za su taimaka mata wajen bude asusun da yadda za ta raba wa asibitoci kudaden domin tallafawa masu fama da cutar.

Wayar da kan mutane game da cutar

Amina ta ce har yanzu mutane da dama basu san menene cutar daji ba.

Amina ta ce ana iya warkewa daga cutar ta hanyar yin gwajin cutar domin gano cutar da wuri a jikin mutum.

Ta kuma ce akwai allurar rigakafi da ake yi domin kare mata daga kamuwa da cutar dajin dake kama mahaifar mace.

Amina ta ce maganin rigakafin na da tsadar gaske.

Ta ce kungiyar FLAC za ta hada hannu da gwamnati, masu ruwa da tsaki da masu hada maganin rigakafi domin ganin an samar da maganin a farashi mai sauki domin kowa da kowa a kasar nan.

Yaduwar cutar daji a Najeriya

Sakamakon binciken da ‘Globocan statistics’ ya gabatar ya nuna cewa daji na yin ajalin mutum sama da 70,000 a Najeriya duk shekara.

Binciken ya nuna cewa a shekaran 2020 mutum 78,899 suka mutu a dalilin cutar.

Sakamakon binciken Globocan statistics ya nuna cewa cutar ta fi kisan Mata fiye da maza a kasar nan.

A shekarar 2020 maza 34,200 be suka rasu a dalilin kamuwa da cutar kuma ta yi ajalin mata 44,699 a kasar nan.