SHUGABAN ƘASA 2023: ‘Yan takarar APC na jihohin ƙabilar Igbo sun yi taron jiran-gawon-shanun goyon bayan duk wanda ya samu tikiti a cikin su

Waɗansu ‘yan takarar shugaban ƙasa su bakwai daga yankin Kudu masu Gabas da ke nema a ƙarƙashin APC, sun yanke shawarar goyon bayan duk wanda ya samu takarar shugabancin ƙasa a cikin su a zaɓen 2023.
A ƙarshen wannan watan ne dai za a gwabza zaɓen fidda gwani na dukkan jam’iyyu, inda APC da PDP kowace za ta yi na ta zaɓen a Abuja.
‘Yan takarar su bakwai ne su ka sanar da yarjejeniyar goyon bayan wanda ya yi nasara a tsakanin su, bayan tashin su daga taron da su ka yi ranar Lahadi, a gidan Rochas Okorocha a Abuja. Okorocha na ɗaya daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa.
Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu ne ya shugabanci taron.
Okorocha tsohon Gwamnan Jihar Imo ne, kuma Sanata mai ci yanzu. Haka ma tsohon Ƙaramin Ministan Ilmi, Chukwumeka Nwajiuba ya halarci taron.
Akwai kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Ken Nnamani da Uju Ken-Ohanenye, wadda mace ce mai takarar shugaban ƙasa, ta halarci taron.
Amma shi ma Gwamnan Jihar Ebonyi Dave Umahi, an ce ya halarci taron ta hanyar ‘zoom’.
Cikin takardar da su ka fitar bayan taron, sun gode wa ‘yan Najeriya waɗanda su ka nuna goyon bayan su ga takarar shugaban ƙasa ga ‘yan takarar yankin ƙabilar Igbo a 2023, wato “goyon bayan damar yankin Kudu maso Gabas su fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin tutar APC.”
Sun kuma gode wa Shugaba Muhammadu Buhari da APC, ganin yadda su ka tashi haiƙan neman ganin sun haɗa kan Najeriya, ta hanyar rungumar kowa daga yankunan ƙasar nan a tafiyar da gwamnati.”
A baya ma ‘yan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar PDP sun yi irin wannan taro a ranar 9 Ga Afrilu, domin tabbatar da ganin cewa na su ne ya samu takarar shugabancin ƙasa daga yankin Kudu maso Gabas.