Shugaba Buhari ya ce Najeriya bata da wata matsalar da ta wuce ƴan Najeriya

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yayi nuni kan yanayin haɗakar Najeriya, wanda ciki ya kunshi cewa, Sam ko kadan ba Banbancin kabila ko addini bane za’a daura wa laifi, “Sai de laifin mu kanmu,” na rashin nuna Adalci.

Shugaban Ƙasar yayi wannan Magana ne kwanan nan yayin da yake karɓan Membobin kungiyar Magoya bayan Buhari da Osinbajo, wato (Muhammadu Buhari/Osinbajo (MBO) Dynamic Support Group), wanda suka ziyarce shi a Fadar Shugaban Kasa, Abuja, don gabatar mishi da kundin tarin Nasarori da Gwamnatin sa ta cimma a shekaru biyar.
Shugaba Buhari yayi nuni kan yanayi kan gwagwarmaya don neman ayi mishi Adalci a Kotuna, bayan rashin yadda sakamako zaben Shugaban kasa A Shekarun 2003 da 2007 da kuma 2021, ya sallama cewa Mutane da suka yanke hukunci da bai bashi nasara ba sun fito ne daga kabila addini daya fito, yayin kuma da wanɗa suka tsaya masa sun fito ne daga addini da kabila ta daban.
“Matsalar mu ba ta kabila ko addini bace, mu kan mu mune Matsalar,” Shugaba Buhari ya nunar da cewa
Ga kalaman nashi:
“Bayan bayyana ta a gaban Babban Kotu Koli a karo na uku, dana fito nayi magana da wanɗa suke nan a lokacin, na fada musu cewa daga 2003, na shafe watanni 30 a Kotu.
“Shugaban Kotun Daukaka kara, Mutum na farko da aka kirashi bada bahasi game da dan takarar Shugaban kasa a wancen Lokacin, Ajin karatun mu daya dashi a makarantar Sakandare a Katsina. Mun shafe Shekaru 6 dashi a aji guda, Mai Shara’a Umaru Abdullahi.
Shugaban Lauyoyi na Shine Cif Mike Ahamba, mabiyin Darikar Roman Katolika kuma Dan Kabilar Ibo. A Lokacin da Shugaban Kotun ya yanke hukunci cewa mu gabatar da korafin mu, Shaida na yana cikin akwatin sauraron jawabin a Kotu,
“Shugaban Lauyoyi na ya hakikan ce cewar dole sai an aike wasika ga Hukumar Zabe Mai zaman Kanta ta Ƙasa INEC, don ta gabatar da mazaɓu da akayiwa Rijista na wasu jihohi, don tabbatar da cewa sanarwar sakamakon Zaben ba gaskiya bace, ya kasance a adane.
“Yayin da suka yanke Hukunci, wani Dankabilar Ibo, Maragi Mai Shara’a Nsofor, ya bukaci maida martani daga Hukumar Zabe kan wasikar da aka aike musu. Haka kawai suka kore maganar. Don haka ya yanke shawarar ya rubuta kin amincewar sa kan hukuncin. Wannan ya faru ne bayan watanni 27 a kotu.
“Daga nan mun wuce zuwa Kotun Koli. Wanda ya kasance Babban Alkalin Alkalai na ƙasa a Sa’ilin ya kasance Dan Kabilar Hausa/Fulani kamar ni, daga Zaria. Alkalan sun tafi zama kusan na mintuna 30, da suka dawo sai kawai suka ce su tafi hutu. Haka nan suka tafi tsawon watanni Uku. Lokacin da suka dawo daga hutu, bai dauke su tsawon mintuna Goma Sha biyar ba suka kore Shara’ar, suka kore mu.
“A shekarar 2007, wanene Shugaban Alkalai na ƙasa? Kutigi. Nan ma Musulmi daga yankin Arewa. Bayan shafe watanni 8 ku wani abu makamancin haka, ya kore karar tamu.
“Na kawo muku wannan labari ne don ku shaida cewa matsalar mu ba Banbancin Kabila ko addini bace. Matsala ce tamu ta kammu.
“Naki na hakura. Nayi ta kokari na.sanya Babbar Riga bayan abinda ya faru dani a cikin Rigar Soji. Anyi mini wani abu saboda Nima nayi wani abu ga wasu. Ku kun sani. Daga karshe, Ni da kaina an kamani, a aike dani gidan Ƙaso, daga nan aka Rika maida musu da kayakin gwamnati da suka sace, na zauna anan gidan Ƙaso na tsawon Shekaru uku da watanni uku. Wannan fa itace irin Kasar tamu.
“Ina fatan Masana Tarihi da masu Basira zasu rubuta su aje wannan jawabi, saboda abune mai kyau ga yanayin Cigaban Siyasa. Don jikoki da jikokin jikokin mu suga ta yadda muka irin gwagwarmaya da mukasha. Bamufa samu cikin sauki ba kamar yadda wasu ke tunani. Ba kawai don Allah ya bamu farin jini da Arziki bane. Munsha wahala kafin mu kai yanzu.
“Ina kokarin ambaton wadan nan abubuwa ne saboda kun hada kanku guri guda, kunyi amfani da kuɗaɗen ku, da karfin ku, ba tare da wani dafa muku da ni nayi ba. Banada bakin da an muku Godiya data dace nayi, Ina Godiya matuka gare ku da Ƴan Najeriya saboda a shekarar 2019, Na ziyarci dukkanin jihohi, mutane da suka fito don su ganni a Fadin Kasar nan (Saboda na sa daukar da kaina don na bauta wa Najeriya da Ƴan-Nijeriya) su son wannan gaskiyar.
“Na godewa Allah kan cewa sama da Shekaru, bazasu zargeni da karɓan Rashawa ba. Kuma naga komi; nayi  Gwamna nayi Ministan Albarkatun Man Fetur, Shugaban kasa na Mulkin Soja, Shugaban Kasa Mulkin Farar Hula wanda ina zango na biyu, kuma ina godiya kan yadda ba wani ne ya tilasta muku ba, kun hadu ne da kanku, kukayi imfani da karfin ku, lokaci da Arzikin ku, Na gode muku matuka, Ina tabbatar muku cewa Tarihi zai muku Adalci.”
Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.