Gwamna Matawalle bai taɓa shawara da ni zai koma APC ba – Aliyu, Mataimakin Gwamnan Zamfara

Mataimakin Gwamnan Zamfara, Mahdi Aliyu, ya tabbatar da cewa Gwamna Bello Matawalle bai taɓa shawara da shi ko sau ɗaya ba cewa zai koma PDP.

A wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa, ya shaida cewa shi ya na nan daram, ba zai ci amanar jam’iyyar PDP ba, saboda haka ba zai canja sheƙa ya bi Gwamna cikin APC ba.

“Ba zan manta yadda aka yi har Allah ya kawo mu a wannan matsayi albarkacin PDP ba.”

Ya ce kuma zai ci gaba da aikin sa lafiya ƙalau tare da Gwamna, har wa’adin zangon farko ya ƙare a 2023.

“Gaskiya ni dai ko sau ɗaya daidai da rana ɗaya bai taɓa tuntuba ta ko neman shawara ta, ko sanar da ni cewa zai canja sheƙa zuwa PDP ba.

“Yadda kowa ke ji a gari, ni ma haka na riƙa ji. Sai yau ranar 29 Ga Mayu da ya yi wanka ya koma APC, na tabbatar.”

Aliyu ya ce zai ci gaba da gudanar da ayyukan sa a matsayin sa na Mataimakin Gwamna, kamar yadda doka ta ba shi ikon yi.

An tambaye shi batun kai ƙara kotu, sai ya ce ai ba shi ke da ikon kai ƙara na.

“Uwar jam’iyya ta ƙasa ce ke da ikon kai ƙara. Saboda haka idan ta duba ta ga akwai buƙatar ta kai ƙara domin a bi mata haƙƙin ta, sai ta nema a kotu.

“Amma dai ni ba zan taɓa ficewa na bar PDP ba. A ƙarƙashin ta mu ka hau mulki, kuma ni dai a ƙarƙashin ta zan sauka.”