Shin irin kwayoyin ‘Bakteriya’ da ake samu a madara ‘Yoghurt’ daidai yake da wanda ake samu a gaban mace? – Binciken Likitoci

Wasu masana daga kasar Amurka sun gudanar da bincike domin gano ko kwayoyin ‘Bakteriya’ da ake samu a madarar ‘Yoghurt’ iri daya suke da wanda ake samu a farjin mace.

Sakamakon binciken da suka gudanar ya nuna cewa kwayoyin ‘Bakteriya’ dake madarar ‘Yoghurt’ da farjin mace ba iri daya bane duk da cewa suna kama da juna.

A cikin madarar ‘Yoghurt’ ana samun kwayoyin ‘Bakteriya’ irin su Lactobacillus bulgaricus da Streptococcus thermophiles amma kuma a farjin mace ana samun kwayoyin bacteriya irinsu Lactobacillus crispatus, Lactobacillus jensenii, Lactobacillus iners, Lactobacillus gasseri da dai sauran su.

Bisa ga tsari ana amfani da kwayoyin ‘Bakteriya’ na Lactobacillus bulgaricus da Streptococcus thermophilous a cikin madara domin madaran ya ɗan yi tsami da kauri. Idan ba irin wadannan kwayoyin ‘Bakteriya’ din aka Yi amfani da su Madara bayan zama ‘Yoghurt’

Su kuma kwayoyin Bakteriya da ke gaban mace na taimaka mata wajen inganta gaban ta da kareta daga kamuwa da cututtuka.

A bayanin da ya yi wani farfesan ‘Microbiology’ a jami’iyyar Western Ontario dake kasar Canada Gregor Reid ya ce duk da cewa kwayoyin ‘Bakteriya’ dake cikin madara ‘yoghurt’ da wandanda ake samu a gaban mace na kama da juna akwai bambamci matuka.

A ƙarshe Reid ya ce kwayoyin ‘Bakteriya’ dake cikin madarar ‘yoghurt’ da Wanda ke farjin mace na da kama amma suna da banbanci sannan idan har aka sauya su ba za su iya yin aikin da ya kamata su yi bisa ga tsari ba yadda suke a kimiyya.