KIBIYAR AJALI: An ƙone wanda ake zargin ya saci wayar hannu ƙurmus

Wani matashi mai shekaru 22 ya gamu da ajalin sa ta mummunar hanya, yayin da mafusata su ka ƙone shi ƙurmus, bayan an zarge shi da satar waya.
Lamarin ya faru a unguwar Atimbo a cikin Calabar, babban birnin Jihar Cross River, a ranar Lahadi.
Wani ganau ba jiyau ba, ya ce sunan wanda aka ƙone ɗin Eyo, kuma ya daɗe ya na ‘yan sace-sace a unguwar, har ta kai an yi masa gargaɗi, amma bai daina ba.
Ganau ɗin ya ce mutumin ya saci wayar a ranar Asabar, aka neme shi aka rasa, sai washegari Lahadi ya koma unguwar.
“Ni fa na san Eyo tun mu na sakandare, a makaranta ma ya yi ƙaurin suna wajen sata, domin akwai ranar da ya sace rabin kuɗaɗen makarantar ‘yan ajin su ƙarƙaf.
“Ko da mu ka fara girma zuwa yanzu da mu ka haura shekaru 20, sai Eyo ya ƙara zama ƙasurgumin ɓarawo. Ba ya gajiya da shirga sata, kuma ba a gajiya da kama shi. Kuma ba yau ne farkon yi masa dukan tsiya a hannun mafusata ba. Yau ɗin ne dai kwanan sa ya ƙare
“Sun fara saran sa da adda, daga nan kuma su ka banka masa wuta. Abin haushin kuma wai waya fa ya sata.” Cewar majiyar mu.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Cross River, Irene Ugbo ta tabbatar da afkuwar lamarin, kuma ta yi tir da waɗanda su ka ɗauki doka a hannun su, su ka kashe shi.
“Kisan da aka yi masa dabbanci ne ƙarara. Kamata ya yi su kai rahoton sa wurin ‘yan sanda.”