Shatu Garko, ƴar jihar Kano ta lashe gasar wacce tafi kowacce mace kyau a Najeriya na 2021

Abin mamaki a gasar wacce ta fi kowa kyau a Najeriya na bana, ƴar jihar Kano, Shatu Garko ce ta cira tuta, inda ta zo ta ɗaya a gasar ta bana.

Wannan shine karon farko da mace da take saka hijabi ta yi nasara a gasar.

Shatu ta doke ƴan mata sama da 1000 da suka shiga gasar duk da ta shiga gasar ne a matsayin ta na bahaushiya ƴar Arewa kuma sanye da hijabin ta a koda yaushe.

Waxce ta yi nasara a gasar ta bana wato Shatu Garko, za ta samu kyautar Naira Miliyan 10, da kyautar sabuwar mota baya ga wasu kyautuka da dama da za ta tafi gida da su.

Nicole Ikot da Kasarachi Okoro ne suka zo na biyu da na uku a gasar