Sanatoci da Mambobin Tarayya za su yi wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe taron-dangi -Sanata Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya ce sanatoci za su zauna tare da mambobin tarayya domin su samu mafita daga ƙin sa hannun da Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙi yi wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe na 2021.

Lawan ya bayyana haka a ranar Laraba a majalisa, kwana ɗaya bayan Shugaba Buhari ya aika masu da wasiƙar ƙin sa wa ƙudirin hannu.

Lawan ya ce a yanzu dai Majalisar Tarayya na hutu, sai watan Janairu za su koma aikin. Don haka da zaran an koma aiki, farkon abin da za su yi, shi ne zaman neman mafita dangane da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe.

Tun a ranar Talata Kakakin Majalisar Tarayya ya bayyana matakin da ya ce za su ɗauka tunda Shugaban Ƙasa ya ƙi sa wa dokar hannu.

Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila ya bayyana irin mataki da Majalisar Tarayya za ta ɗauka, ganin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙi amincewa ya sa wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe Hannu.

A ranar Lahadi ce dai wa’adin kwana 30 su ka cika, domin Buhari ya sa wa dokar hannu ko ya ƙi.

Tun cikin watan Nuwamba aka aika masa da ƙudirin. Sai ranar Talata ce Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya cewa ba zai sa wa ƙudirin hannu ba, saboda batun zaɓen kai-tsaye na ‘yar-tinƙe.

Kakakin Majalisar Tarayya ya ce tunda hutun wata ɗaya za a tafi, Majalisar Tarayya za ta jira sai ta dawo daga hutu sannan ta ga abin da ya fi dacewa ga ƙasar nan.

“Ko ma dai me kenan, kada mu bari garin gyaran doro mu karya ƙugu. Ƙasar nan ce mafi muhimmanci a gare mu.”

A nasa bayanin, Shugaban Marasa Rinjaye Ndudi Elumelu, ya bada shawarar Majalisa ta gaggauta cire batun zaɓen-kai-tsaye a cikin ƙudirin gyaran zaɓen, sai a sake aika wa Buhari a ranar Talata ɗin kafin lokacin tashi aiki, yadda shi Buharin tilas ya sanya wa dokar hannu.

PREMIUM TIMES ta buga labarin iƙirarin da Sanata George Sekibo na PDP ya yi cewa, sama da Sanatoci 73 sun rattaba hannun kafa sabuwar dokar zaɓe ta hanyar bijire wa Buhari.

Sanata George Sekibo ya tabbatar da cewa akwai sama da sanatoci 73 waɗanda su ka sa hannun amincewa su tirsasa Shugaba Buhari su tabbatar da Sabuwar Dokar Zaɓe, wadda Buhari ya ƙi rattaba wa hannu domin ta zama doka.