Sanata Uba Sani ya yi alhinin rasuwar mahaifin Kashim Bukar, ya yi ziyarar ta’aziyya da gaishe-gaishe

Sanata Uba Sanu dake wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa kuma daya daga cikin ƴan takarar gwamnan jihar Kaduna a APC ya yi ziyarar ta’aziyya ga wasu abokan arziki da suka rasa makusantan su a Kaduna.
Tawagar sanatan dai ta fara ne da kai gaisuwar ta’aziyya ga iyalan Kashim Bukar Shettima wanda ya rasa mahaifinsa.
Bayan addu’o’i da aka yi, Allah ya jiƙansa da rahama,
Sanata ya kai ziyara Alh Alimi Yau wand shima ya rasa ɗan sa Mukhtar Alimi.
Bayan haka sai sanatan tare da tawagar sa suka ɗunguma zuwa gidan marigayi Muhammad Sani Aldulmajid (MS Ustaz) wanda daya ne daga cikin waɗanda ibtila’in harin jirgin kasan Kaduna ya riske da.
Idan ba a manta ba a cikin wannan mako ne gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ayyana sanata Uba Sani a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC bayan ya umarci Mohammed Sani Dattijo ya janye wa Uba.