Sai ma’aikata a Abuja sun yi rigakafin Korona za su rika shiga wurin aiki – Hukumar FCTA

Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta bayyana cewa daga ranar 17 ga watan Janairu za ta fara hana ma’aikatan da basu yi allurar rigakafin korona shiga wuraren aikinsu.

Maitaimaka wa ministan Abuja kan harkokin yada labarai Abubakar Sani ya sanar da haka ranar Talata.

Sani ya ce hukumar ta aika da wasikar wannan sanarwan wa duk shugabanin ma’aikatu domin ganin duk ma’aikata dun kiyaye.

Ya ce hukumar ta kuma ce za ta zuba jami’an tsaro a kowace kofa domin hana duk ma’aikatan da basu yi allurar rigakafin ba.

“Wannan dokan ya shafi wadanda za su ziyarci hukumar da su tabbatar sun taho da katin su na yin allurar rigakafin ko kuma sakamakon gwajin cutar korona wanda ya nuna basa dauke da cutar.

Sani ya ce wannan sanarwa na tare da sanarwar da gwamnatin tarayya ta fitar na duk ma’aikatan gwamnati daga rukunin 12 zuwa ƙasa su koma aiki daga ranar 1 ga Disemba 2021.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya gwamnatin tarayya ta sanar cewa duk ma’aikatan gwamnati su je su yi allurar rigakafin korona.

Gwamnati ta kuma ce ma’aikata za su dawo kan aikinsu idan sun gabatar da katin yin allurar rigakafin cutar ko Kuma sun gabatar da sakamakon gwajin cutar wanda ya nuna basa dauke da cutar.kokin gujewa kamuwa da cutar tare da yin allurar rigakafin cutar domin dakile yaduwar cutar.