RIKICIN ‘YANCIN KOTUNA: Gwamna Wike ya yi fatali da yarjejeniya tsakanin Ƙungiyar Gwamnoni da Ƙungiyar Ma’aikatan Kotu

Gwamnan Jihar Rivers, Nysom Wike ya bayyana cewa Jihar Rivers ko kaɗan ba ta amince da yarjejeniyar da Kungiyar Gwamnonin Najeriya (GFN) ta cimma tsakanin ta da Ƙungiyar Ma’aikatan Kotunan Najeriya (JUSUN) ba.

“Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya ƙungiya ce kawai ta zama a yi musayar ra’ayi da tattauna batutuwa a tsakanin gwamnonin Najeriya. Don haka ba ta da wani ƙarfin ikon da za ta zartas da wata doka a madadin sauran ɗaukacin jihohin Najeriya ko madadin sauran gwamnonin Najeriya.

“Kungiyar Gwamnoni ba fa gwamnati ba ce. Kawai ƙungiya ce ta zama ana tattauna barutuwa, ba wai ta sa hannu kan wata yarjejeniya a madadin sauran jihohi ko sauran gwamnonin Najeriya.”

Haka dai Wike ya furta a taron bude ginin Majalisar Jami’ar Jihar Rivers a Fatakwal, kamar yadda Kakakin Yaɗa Labarai na Wike, Kelvin Ebiri ya sanar a cikin wata sanarwa da ya citar.

“Kai ni fa yadda na kan yi, ko wani abu aka tattauna ko ƙungiyar gwamnoni su ka faɗa, to sai na fara dawowa jiha ta tukunna mun tattauna barun a Majalisar Zartaswa, tare da dukkan kwamishinoni na mun duba batun. Sannan mu zan abin yi ko mataki na gaba da za mu ɗauka.

“Saboda haka duk ma wata yarjejeniyar da Kungiyar Gwamnoni ta cimma da JUSUN, to su je can su ƙare ta, babu ruwan Gwamnatin Jihar Rivers da yarjejeniyar.”

Wike ya ce tuni bangaren shari’a da Majalisar Dokokin Jihar Rivers su na cin gashin kan su.Don haka ba zai amince da yarjejeniyar da Kungiyar Gwamnonin Najeriya su ka cimma da JUSUN ba.

Ya ce tuni har ma bangaren shari’a na Jihar Rivers ya karbi kudin sa na watanni shida. Saboda haka babu ruwan jihar da wata yarjejeniya kuma.

“Baya ga kuɗaɗen haƙƙin su da mu ke ba su, kuma har ayyukan raya ƙasa mu ke kashe wasu kuɗaɗen mu ke yi masu.”