RIKICEN APCn KANO : Hadimin Ganduje ya koma tsagin Shekarau, ya ajiye mukaminsa

Mai baiwa gwamna Abdullahi Ganduje shawara kan harkokin da suka shafi Jiha, Muhammad Shehu, ya ajiye mukaminsa kuma ya koma tsagin Sanata Ibrahim Shekarau.

Hakan yana faruwa ne a ci gaba da rikicin cikin gida da ya dabibaye Jam’iyyar APCn reshen Jihar Kano.

Shi dai Gwamna Ganduje yana goyon bayan shugabancin Abdullahi Abbas, Malam Shekarau wanda shi ne Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, yana bangaren Ahmadu Danzago.

Bayan yayi taro da magoya bayansa ranar Talata, a Karamar Hukumar Nasarawa, hadimin na Ganduje, Malam Shehu, ya bayyanawa Yan Jarida cewa ya dawo bangaren Shekarau da dubban magoya bayansa saboda rashin iya shugabanci irin na bangarensu Abdullahi Abbas.

Yace shugabancin Abdullahi Abbas ya fifita wane bangare na Jam’iyyar APCn Karamar Hukumar Nasarawa duk da cewa shi ne jagora mai tarin magoya ‘yan jam’iya a Nasarawa.

Malam Shehu yace sun dawo bangaren Shekarau ne domin su taimakawa tafiyar siyasar sanata Barau Jibrin, mai neman takarar gwamna a Kano a Shekarar 2023.

A yanzu Barau Jibrin shi ne sanata mai wakiltar Kano ta Arewa.

Malam shehu shi ne jami’in gwamnati na farko da ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga tsagin Shekarau tun bayan da kotu ta kore shuwagabannin jam’iya da Abdullahi Abbas ya ke yi wa jagoranci.