Dattawan Zamfara sun zargi jami’an tsaro da sakin ‘yan bindigar da ke tsare

Wasu gungun dattawan Jihar Zamfara sun yi kururuwar nuna damuwar su a kan sakin gaggan ‘yan bindiga da masu haɗin baki da su, waɗanda su ka zargi jami’an tsaro ke saki a jihar.

Dattawan sun yi kira ga jami’an tsaro su daina sakin ‘yan bindigar da ‘yan-koren su, kuma su ka ƙara da cewa sakin su da ake yi ɗin ne ke ƙara munin matsalar tsaron da Zamfara ke fama da ita.

A taron da dattawan su ka yi a Gusau babban birnin jihar ne su ka bayyana wannan damuwa. Sannan kuma sun nuna takaicin su dangane da halin ƙuncin da marayun da aka kashe wa iyaye ke ciki, waɗanda yawancin su duk yara ne ƙanana ƙwarai.

Tsohon Sanata, Sa’idu Ɗansadau ne ya yi wa manema labarai taƙaitaccen bayani bayan sun kammala taron.

“Wannan kwamiti na dattawan Zamfara ya na mai nuna matuƙar ɓacin rai ganin yadda jami’an tsaro ke sakin ‘yan bindigar da aka kama. Ya ce jami’an da ke sakin ‘yan bindigar ko dai waɗanda suka kamo su ke saki, ko kuma waɗanda sojoji su ka kamo su ka damƙa masu. Ko kuma waɗanda ‘yan bijilante su ka kamo su ka damƙa masu.” Inji Ɗansadau.

“Muna kira ga jami’an tsaro na cikin jihar nan, don Allah, ku daina sakin ‘yan bindigar da ake kamowa. Ku riƙa gurfanar da su a kotu. Saboda sakin maharan nan bagatatan da ake ta yi, shi ne ya ƙara rura wutar kashe-kashe baya-bayan nan a Zamfara.”

Ɗansadau ya nemi sake farfaɗo da ƙungiyoyin kishin al’umma na cikin jama’a, domin su nemi gudummawar gina makarantun firamare da na sakandare ga ƙananan yaran da ‘yan bindiga su ka kashe wa iyaye, su ka maida su marayu.

Ɗansadau ya ce an samu ƙarin tsaro a Zamfara, lokacin da aka kulle wayoyin sadarwa a jihar Zamfara.

Sai dai kuma ya ce wurare irin su Birnin Magaji, Shinkafi da Ƙaramar Hukumar Zurmi har yanzu ‘yan bindiga na shigar su kai-tsaye.

Mambobin wannan kwamiti sun ƙunshi sarakunan gargajiya, manyan mutanen cikin jihar, malaman addinin musulunci da wasu masu ruwa da tsaki a siyasar jihar Kaduna, su ne su ka haɗa taron musulmai da kiristoci domin a yi addu’ar samun zaman lumana a faɗin jihar.

Sai dai kuma Kwamishinan Harkokin Tsaro Mamman Tsafe, ya ce zargin da dattawan suka yi abu ne mai iya kashe guyawun jami’an tsaron.

Sai dai kuma ya ce duk da haka dai zai bincika ya ga shin wannan zargin idan ya na da ƙamshin gaskiya a cikin sa.