RAWA MA DA RANAR TA: An rantsar da gwanin rawa Adeleke Gwamnan Osun, har ya kulle dukkan asusun ajiyar gwamnatin jihar zai yi bincike

An rantsar da Ademola Adeleke na PDP sabon Gwamnan Jihar Osun a ranar Lahadi. An rantsar da shi da Mataimakin sa a filin wasa na Osogbo, babban birnin jihar a gaban dubban magoya bayan sa.
Jim kaɗan bayan rantsar da shi, Adeleke ya bayyana cewa ya kulle dukkan asusun gwamnatin Jihar Osun, kada wanda ya ƙara kashe ko sisi.
Sannan kuma ya ce zai kafa kwamitin binciken da zai gano yawan kadarorin gwamnati da jami’an gwamnatin da ya gada su ka arce da su, domin a gaggauta ƙwatowa.
Ya zargi tsohon gwamnan da ya sauka, Gboyega Oyetola da almubazzaranci da kuma bushasha da dukiyar al’umma.
“Wani abin takaicin kuma shi ne, Oyinlola ya riƙa ɗaukar ma’aikata birjik a lokacin da ya kusa tafiya, don kawai ya haɗa ni husuma da su idan na hau.
“Saboda ya san babu kuɗin da za a biya su albashi, kuma ba a ma tsara masu albashin ba tukunna, amma ya riƙa ɗaukar mutane aiki kawai.”
Ya ce duk wanda ya yi gaba da kadarorin gwamnati sai an bi shi an ƙwato abin da ya gudu da shi, ko kuɗi ko kadarori.
Yadda Gwanin Rawa, Adeleke Ya Zama Gwamnan Osun:
Cikin watan Yuli ne aka gudanar da zaɓen gwamnan Osun, inda gwanin rawa, kawun Davido ya farfasa gangunan Buhari, Tinubu, APC da Oyetola ya lashe zaɓen gwamna.
A lokacin, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta bayyana Ademola Adeleke na PDP cewa ya yi nasara a zaɓen gwamnan Jihar Osun.
Da ya ke sanarwar a safiyar Lahadi, Baturen Zaɓe na Jihar Osun Oluwatoyin Ogundipe, ya bayyana cewa, “Ademola Adeleke na PDP ya samu ƙuri’u 403, 371. Shi kuma Gwamna Gboyega Oyinlola ya samu 375, 027.”
“Saboda ka samu yawan waɗannan ƙuri’u, to ka cika sharuɗɗan cin zaɓe. Don haka kai ne ka yi nasarar zaɓen gwamnan jihar Osun, wanda aka yi ranar Asabar, 16 Ga Yuli, 2018.
Baya ga lashe zaɓen, Adeleke ya yi nasara a Ƙananan Hukumomi 17 daga cikin 30 da ke jihar. APC ta samu ƙananan hukumomi 13.
Sauran jam’iyyu 13 kuwa babu wadda ta samu ko ƙaramar hukuma ɗaya.
Ramuwar Gayyar Kwankwatsar Da Su Tinubu Su Ka Yi Wa Adeleke A 2018:
Zaɓen gwamnan Osun rayuwar gayya ce Adeleke ya yi kan Oyetola, Tinubu da Shugaba Muhammadu Buhari, da kuma APC kacokan.
A zaɓen 2018, APC ta cika Osun da gwamnoni da jiga-jigai, inda aka kayar da Adeleke na PDP, bayan an yi zaɓen ‘inkwankilusib’.
An yi wa Adeleke taron dangi, inda har aka haɗa da wasu jam’iyyu, domin a kayar da Adeleke a wata rumfar zaɓe ɗaya tal.
Zaɓen yanzu na 2022 kuwa alama ce mai nuna cewa ɗan takarar APC a zaɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu zai sha wahala a yankin sa na Kudu maso Yamma. Tunanin da ake yi cewa zai kwashi miliyoyin ƙuri’u a ɓagas, zaɓen Osun ya nuna ba haka siyasar za ta kasance ba.
Mulkin Adeleke zai fara ne daga watan Nuwamba, sadda wa’adin gwamnan da ya sha kaye zai ƙare.
Zaɓen ya ƙara zama tarihin da ɗan takara ya kayar da gwamna wanda ke kan mulki, kuma wanda jam’iyyar sa APC ke mulki a ƙasa.
PDP ta ƙwace jihar Osun, makonni uku bayan ta kasa ƙwato jihar Ekiti daga APC.