QATAR 2022: Amurka Ta Kimtsa Ko Ta Doke Iran Ko Kuma Ta Tattara Ta Koma Gida

Kimanin shekaru 24 kenan da Amurka ta fafata da kasar Iran. A waccan lokacin Amurka bata ji da dadi ba a wasan da ta yi da Iran a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a kasar Faransa a shekarar 1998, inda Iran ta doke Amurka da ci 2-1, lamarin da ya yi sanadiyar ficewar Amurka daga gasar.