RASHIN TSARO: Majalisa na bukatar a gaggauta kara jami’an tsaro a makarantu

Majalisar Tarayya ta shaida wa Gwamnatin Tarayya ta fito da wani sabon tsarin inganta tsaro a makarantun fadin kasar nan.

Dan Majalisar Jam’iyyar PDP, Benjamin Mzondu da Julius Ihonvhere, dan APC daga Edo ne su ka gqbatar da korafin a ranar Talata, lokacin zaman Majalisa.

Makarantun sakandare, kwalejoji da jam’a duk sun dandana zafin matsalar tsaro a cikin shekarun nan.

Na baya-bayan nan su ne daliban Islamiyya 139 da ‘yan bindiga su ka sace a garin Tegina, Jihar Neja.

A ranar Talata din nan ‘yan Majalisar su biyu sun bayyana cewa, “Irin yadda ake yawan shiga makarantun kasar nan ake sace dalibai da malaman su, ya na nufin irin gagarimar matsalar tsaron da kasar nan ke fama da ita.

Alkawarin Buhari Kan Tsaro: A cikin Kundi ko Daftarin Manufofin APC a lokacin kamfen kafin zaben 2015, jam’iyyar APC ta yi alkawarin cewa idan ta ci zabe a 2015, za ta bi ilahirin makarantun Arewa maso Gabas duk za a killace su, ta hanyar kewaye su da katanga, da waya da kuma kyamara mai gani har hanji (wato CCTV).

Sai dai kuma shekaru shida kenan da APC ta hau mulk, amma ko sake tayar da zancen ba a sake yi ba.