CAKWAKIYA: Kakakin jam’iyar APC a jihar Kebbi ya yi murabus

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Sakataren yaɗa labaran jihar Kebbi, Alhaji Sani Dodo (Tambarin Gwandu) ya sanar da ajiye muƙaminsa a yau Talata.

Dododo, ya sanar da matsayr nasa ne a wani gajeren bidiyo da Hausa Daily Times ta samu, yana mai cewa ya ajiye muƙamin ne ba tare da tirsasawa ba ko wani dalili.

A cikin Bidiyo ya miƙa godiyansa ga magoya bayan jam’iyar APC na jihar Kebbi da suka bashi goyon baya a iya lokacin da ya ɗauka yana Sakataren watsa labaran jam’iyar APC mau mulki a jihar.

Sai dai mutane sun fara tunanin akwai wani abu a ƙasa domin a haka kawai Alhaji Sani Dododo ba zai ajiye muƙaminsa ba duba da irin rawa da yake takawa a gwamnatin Abubakar Atiku Bagudu.